Gurfanar da alkalin alkalai: Atiku ya bawa Buhari shawara

Gurfanar da alkalin alkalai: Atiku ya bawa Buhari shawara

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya ce duk wani uzuri da gwamnatin tarayya zata yi amfani da shi domin kawar da alkalin alkalai na kasa, Walter Onnoghen, daga ofis za a bashi wata ma'ana ta daban.

Dan takarar na wadannan kalamai ne a matsayin martani ga karar da hukumar da'ar ma'aikata (CCB) ta kai Onnoghen.

A yau, Asabar ne, shugaban sashen yada labarai na kotun da'ar ma'aikata (CCT), Ibraheem Al-Hassan, ya bayyana cewar a ranar Litinin ne za a gurfanar da Onnoghen a gaban kotusu.

Za a gurfanar da alkalin alakalan ne bayan wani rubutaccen korafi da aka yi a kansa.

Sai dai, a wani jawabi, Atiku ya ce duk wani yunkurin taba Onnoghen zai kara rura wutar zargin cewar Muhammadu Buhari na son yin raba shi da kujerar sa ne saboda zabe mai zuwa.

Gurfanar da alkalin alkalai: Atiku ya bawa Buhari shawara

Atiku da Buhari
Source: Twitter

Atiku ya kara da cewar kamata ya yi wata kotu mai cikakke iko ta saurari karar da aka shigar da Onnoghen, amma ba kotun gwamnatin Buhari ba.

"Ni kaina na shiga cikin sahakku bayan samun labarin cewar za a gurfanar da alkalin alkalai na kasa, Walter Onnoghen, a gaban gaban kotun da'ar ma'aikata, musamman ganin cewar zabe na kara matsowa.

DUBA WANNAN: Jigo a APC ya bawa Buhari kyautar zungureriyar motar kamfen, hoto

"Abinda ya kara karfafa zargin da nake yi shine yadda gwamnatin Buhari ke kokarin tursasa bangaren gwamnati mai cin kashin kansa domin saka Onnoghen yin murabus.

"Ina bukatar a yi wa Onnoghen adalci tunda har yanzu ba a tabbatar da laifin da ake zargin shi da aikata wa ba," a cewar Atiku.

Kazalika, Atiku ya bukaci a tuhumi Onnoghen a kotu mai cikakken iko, ba gwamnatin Buhari ba tare da yin kira ga shugaban kasa da ya kasance mai biyayya ga doka a duk abinda zai yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel