Gurfanar da alkalin alkalai: Gwamnonin yankin kudu maso kudu sun kira taron gaggawa

Gurfanar da alkalin alkalai: Gwamnonin yankin kudu maso kudu sun kira taron gaggawa

Gwamnonin yankin Kudu maso Kudu na Najeriya sun kira taron gaggawa domin tattaunawa a kan rahoton da suka ji na cewa gwamnatin tarayya na shirin tsige alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen daga kujerarsa.

The Cable ta ruwaito cewa gwamnonin karkashin kungiyar gwamnonin Kudu maso Kudu za su tattauna wasu batutuwa ciki har da kallubalen tsaro a yankin Neja Delta a yayin zabe da bayan zabe, kason arzikin kasa da kuma batun gurfanar da alkalin alkalan Najeriya a gaban kotu.

Gwamna Seriake Dickson ya sanar da bakin hadiminsa, Fedelis Soriwei a yau Asabar 12 ga watan Janairu cewa bai samu cikaken bayani daga Kotun Koli na kasa ba game da Alkalin Alkalan sai dai ya yi gargadin cewa tayar da wannan batun gabanin zabe abu ne mai hadari.

DUBA WANNAN: Jihohi 10 da suka fi bunkasa a Najeriya a yanzu

Zargin tsige Alkalin Alkalai: Gwamnonin Kudu sun kira taron gaggawa

Zargin tsige Alkalin Alkalai: Gwamnonin Kudu sun kira taron gaggawa
Source: UGC

Gwamnan ya ce kungiyar gwamnonin Kudu maso Kudu za ta sanar da matsayar ta a kan batun da kuma matsayan al'ummar yankin bayan sunyi taron.

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewar gwamnatin tarayya ta bukaci Alkalin Alkalan na Najeriya, Justice Walter Samuel Nkanu Onnoghen ya sauka daga kujerarsa a matsayin shugaban fanin Shari'a a Najeriya saboda rashin bayyana kadarorin da ya mallaka.

A cewar Vanguard, gwamnatin tarayya zata gurfanar da Alkalin Alkalan a gaban kwamitin bincike na musamman karkashin jagorancin Justice Danladi Yakubu a ranar Litinin 14 ga watan Janairu a Abuja.

Jaridar ta ce ana zargin Alkalin Alkalan ne da laifin rashin bayyana kadarorinsa kamar yadda doka ta tanada da kuma amfani da asusun ajiya na ajiye kudaden kasashen waje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel