Rundunar 'yan sanda ta kama wata motar daukan kaya makare da alburusai 34,865

Rundunar 'yan sanda ta kama wata motar daukan kaya makare da alburusai 34,865

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Ogun tayi nasarar kama wata karamar motar daukan kaya dauke da kwanson alburusai da yawansu ya kai 34,865 a wata iyakar Najeriya da kasar Togo dake jihar Ogun.

An kama motar a iyakar dake garin Ilara kuma bincike ya gano cewar za a kai makaman garin Onitsa na jihar Anambra bayan an shigo dasu daga Jamhuriyar Benin.

Kazalika rundunar 'yan sanda ta cafke wasu mutane, cikinsu har da dan kasar Togo, da ake zargin nada hannu cikin shigo da makaman. Wadanda aka kama din sune; Isah Muhammad (dan kasar Togo, sai kuma 'yan Najeriya; Alabi Fayemi da Seyi Bamgbose.

Rundunar 'yan sanda ta kama wata motar daukan kaya makare da alburusai 34,865

Rundunar 'yan sanda ta kama wata motar daukan kaya makare da alburusai 34,865
Source: Twitter

Kwanson alburusai 34,865
Source: Twitter

Rundunar 'yan sanda ta kama wata motar daukan kaya makare da alburusai 34,865

Wadanda ake zargi da safarar alburusai
Source: Facebook

Jam'ian rundunar 'yan sanda dake binciken ababen hawa a kan hanya ne suka kama motar a garin Olohunda dake kan iyakar kananan hukumomin Abeokuta ta Arewa da Afon.

DUBA WANNAN: Yadda Buhari da IBB suka tilasta min barin soja - Kaftin Bala Shagari

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama wasu mahauta hudu da ke sayar da nama a Agege na jihar Legas bisa zarginsu da daukan nauyin 'yan bindiga da ke kai hare-hare a wasu garuruwa a jihar Zamfara.

The Punch ta ruwaito cewa garuruwan da aka kai harin sun hada da kananan hukumomin Tsafe, Zurmi, Shinkafi, Maradun, Mari da Birnin Magaji.

'Yan sandan sunyi ikirarin wadanda ake zargin su ke samarwa 'yan bindigan kudaden da sukae sayan makamai ta hanyar sayan shanun sata daga hannunsu. Wadanda ake zargin sune Alhaji Ago Atine, Alawani Abubakar, Mohammad Sahagari da Bashir Aliyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel