Jigo a APC ya bawa Buhari kyautar zungureriyar motar kamfen, hoto

Jigo a APC ya bawa Buhari kyautar zungureriyar motar kamfen, hoto

Jamilu Gwamna, Jigo a jam'iyyar APC kuma tsohon dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, ya bayar da kyautar wata zungureriyar mota a matsayin gudunmawar yakin neman zabe ga Buhari da dan takarar gwamna a jihar Gombe, Alhaji Yahaya Inuwa.

Da yake magana da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) bayan mika kyautar motar a Gombe, Gwamna ya ce Buhari da Inuwa na bukatar gudunmawa daga wurin 'yan Najeriya masu kishi.

A cewar sa, 'yan Najeriya na bukatar shugabannin masu kishi da tsantseni wajen kashe dukiyar al'umma.

"Shugaba Buhari da Alhaji Inuwa 'yan takara ne da zasu kawo cigaban da jama'a ke bukata a Najeriya da jihar Gombe.

"Wadannan 'yan takara biyu na da gaskiya da rikon amana. Irinsu ne shugabannin da Najeriya ke bukata a irin wannan lokaci da ake bukatar shugabanni masu kishin jama'a.

Jigo a APC ya bawa Buhari kyautar zungureriyar motar kamfen, hoto

Jigo a APC ya bawa Buhari kyautar zungureriyar motar kamfen
Source: Facebook

"A cikin shekaru kusan hudu da shugaba Buhari ya yi yana mulki, ya taba rayuwar 'yan kasa ta hanyar bullo da shirye-shirye daban-daban domin tallafawa talaka.

"Kudin da shugaba Buhari ya yi amfani da su wajen tallafawa matasa 500,000 a shirin N-power, da sace su za a yi ba don shine ke mulki ba," a cewar Gwamna.

DUBA WANNAN: An yi harbe-harbe yayin da wasu matasa suka yi yunkurin rushe ofishin kamfen din Atiku

Gwamna ya bukaci jama'ar jihar Gombe su kada kuri'unsu ga shugaba Buhari da Alhaji Inuwa domin samun shugabanci nagari.

A ranar 2 ga watan Oktoba na shekarar 2018 ne Gwamna ya canja sheka daga PDP zuwa APC bayan ya rasa takarar kujerar gwamna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel