Yadda Buhari da IBB suka tilasta min barin soja - Kaftin Bala Shagari

Yadda Buhari da IBB suka tilasta min barin soja - Kaftin Bala Shagari

Captain Muhammad Bala Shagari (mai ritaya), hakimin garin Shagari kuma babban dan marigayi Shagari, ya yi tsokaci a kan rayuwar mahaifinsa da ya rasu sati biyu da suka wuce tare da yin waiwaye a kan yadda ya fuskanci matsin lamba a cikin aikin soji bayan an yiwa mahaifinsa juyin mulki, yayin wata hira da ya yi da jaridar TheSun dake fitowa kowacce ranar Asabar.

Da yake amsa tambayar shin ko yana ina lokacin da aka yiwa mahaifinsa juyin mulki, Captain Bala Shagari, sai ya ce, "lokacin da aka zabi mahaifina shugaban kasa tuni na kai matsayin Laftanal a rundunar soji, lokacin ina Legas domin wani aiki na musamman.

"Da yake a lokacin da kotu ta tabbatar da mahaifina a matsayin shugaban kasa bayan yanke hukunci tsakaninsa da Awolowo, a daidai lokacin ne aka yin karin girma zuwa Laftanal, ba zan manta ba saida kwamanda na ya zoloyen cewar 'mahaifinka ne sabon zababben shugaban kasa, kai kuma sabon zababben Laftanal.

Yadda Buhari da IBB suka tilasta min barin soja - Kaftin Bala Shagari

Kaftin Bala Muhammad Shagari
Source: Twitter

"Har zuwa lokacin da aka yiwa mahaifina juyin mulki ina aiki soja kafin daga baya gwamnatin Buhari tayi min ritayar dole.

DUBA WANNAN: Rayuwata tana cikin hatsari - Bukola Saraki

Da aka tambayi Kaftin Shagari me yasa aka yi masa tiyatar dole, sai ya kada baki ya ce, "babu wani dalili, kawai saboda ni da ne ga tsohon shugaban kasa Shagari. Ba zan taba manta abinda aka rubuta a wasikar yi min ritayar ba 'bisa ikon da nake da shi a matsayina na shugaban rundunar soji da tsaro ta kasa, nayi maka ritaya daga aiki kuma bama bukatar gudunmawar ka a cikin aikin soji'."

Kaftin Bala Shagari ya ce sakataren tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ne ya saka hannu a kan wasikar lokacin IBB na rike da mukamin shugaban rundunar sojoji da tsaro na Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel