Atiku ya fadi matakin da zai dauka a kan 'yan Boko Haram da aka kama

Atiku ya fadi matakin da zai dauka a kan 'yan Boko Haram da aka kama

- Dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar ya ce ba dai-dai bane a rika sakin gawurtattun masu laifi da suka kashe sojojin Najeriya

- Atiku ya yabawa Kungiyar dattawan Borno kan kirar da su kayi da shugaba Buhari ya dena sakin tubabbun 'yan Boko Haram

- Dan takarar shugaban kasar ya yi kira ga Buhari ya magance makiyan Najeriya da ba tare da ya nuna alamar gazawa ba

Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce idan aka zabe shi shugaban kasa ba zai saki tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram ba saboda za su iya komawa su cigaba da kashe Sojojin Najeriya.

A sanarwar da ya fitar da bakin mai magana da yawunsa, Paul Ibe a ranar Asabar 12 ga watan Janairu, dan takarar shugaban kasar ya ce babu wani hikima ko dabarun yakin soji cikin sakin gawuratattun 'yan ta'adda da suka kashe dakarun soji.

Ba zan taba sakin tubabun 'yan Boko Haram ba idan na zama shugaban kasa - Atiku

Ba zan taba sakin tubabun 'yan Boko Haram ba idan na zama shugaban kasa - Atiku
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Legas: An kama manyan 'yan kasuwa dake daukar nauyin 'yan bindigar Zamfara

Ya yabawa Kungiyar dattawan Jihar Borno saboda kirar da su kayi ga Shugaba Muhammadu Buhari ya dena sakin tubabbun mayakan Boko Haram kamar yadda The Tribune ta ruwaito.

"Babu wani hikima tattare da sakin gawuratattun 'yan ta'adda wadda suka kashe rayukan sojojin Najeriya wai da sunan sun tuba kuma an canja masu tunani," inji Sanarwar.

"Kamar yadda Atiku ya fadi a bara, duk wani mai hankali zai lura cewa an samu karuwar hare-haren kungiyar Boko Haram/ISWAP ne a daidai lokacin da gwamnatin Buhari ta bullo da shirin sakin tubabbun 'yan ta'addan.

"Atiku ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya tuna abinda tsohon kwamandan Boko Haram, Abba Umar ya fadi yayin da aka kama shi na cewa muddin aka sake shi zai koma dajin Sambisa ne."

Har ila yau, Atiku ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi maganin makiyan Najeriya ba tare da ya nuna wani nau'in gazawa ba domin hakan zai kara wa 'yan ta'addan kwarin gwiwa ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel