Yanzu-Yanzu: Wani dan majalisar tarayya daga Arewa ya fita daga APC zuwa PDP

Yanzu-Yanzu: Wani dan majalisar tarayya daga Arewa ya fita daga APC zuwa PDP

Dan majalisar tarayya dake wakiltar mazabar kananan hukumomin Jos ta kudu da ta gabas a jihar Filato mai suna Edward Pwajok (SAN) ya sanar da komawar sa jam'iyyar adawa ta People’s Democratic Party (PDP) daga All Progressives Congress (APC) tare da magoya bayan sa.

Hon. Pwajok wanda ke zaman shugaban kwamitin tsare tsare na majalisar ta wakilai ya bayar da wannan sanarwar ne a ranar 12 ga watan Janairu lokacin da tara daruruwan magoya bayan sa a gidan sa dake a garin na Jos.

Yanzu-Yanzu: Wani dan majalisar tarayya daga Arewa ya fita daga APC zuwa PDP

Yanzu-Yanzu: Wani dan majalisar tarayya daga Arewa ya fita daga APC zuwa PDP
Source: UGC

KU KARANTA: An kama mai kera bindigu a Zamfara

Legit.ng Hausa ta samu cewa dan majalisar dai yayiwa jam'iyyar ta APC tattas inda yace ya gama nazari ya kuma gano cewa babu wani abun kirkin da zai taba fitowa daga jam'iyyar.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa dan majalisar wanda daya daga cikin na hannun damar dan takarar shugaban kasa ne na jam'iyyar PDP a zaben na 2019, Atiku Abubakar a baya ya fita daga PDP ya koma APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel