Tsaka mai wuya: An sake canjawa Dino wuri daga asibitin DSS

Tsaka mai wuya: An sake canjawa Dino wuri daga asibitin DSS

Rundunar 'yan sandan Najeriya sun dauke Sanata Dino Melaye daga asibitin DSS zuwa ofishin rundunar 'yan sandan masu hana fashi da makami (FSARS) da ke Guzape a Abuja.

A jiya Juma'a ne 'yan sandan suka kai Sanata Melaye asibitin DSS da ke Abuja domin a duba lafiyarsa bayan ya koka cewa baya jin dadin jikinsa.

Bayan kai shi asibitin na DSS, 'yan sanda sun tabbatar da cewa ya samu sauki da za iya fuskantar bincike a yanzu.

Da duminsa: 'Yan sanda sunyi awon gaba da Dino zuwa ofishin SARS

Da duminsa: 'Yan sanda sunyi awon gaba da Dino zuwa ofishin SARS
Source: UGC

Wani na kusa da Sanatan ya shaidawa The Cable cewa babu wanda ya san matakin da 'yan sandan za su dauka.

DUBA WANNAN: Jihohi 10 da suka fi bunkasa a Najeriya a yanzu

"Sunyi dauke shi zuwa ofishin SARS da ke Guzape. Ba su ce da kowa uffan ba lokacin da za su tafi dashi. Ba mu san abinda za su aikata ba yanzu," inji hadimin Dino.

A dai makon da ya gabata ne Melaye ya mika kansa ga 'yan sanda bayan sun kwashe kwanaki takwas suna girke a kofar gidansa.

Ana zarginsa ne da hannu cikin yunkurin kashe wani dan sanda mai suna Danjuma Saliu wadda aka harba a ranar 19 ga watan Yulin shekarar 2018 a jihar Kogi.

Ya ce, "ana binciken Melaye ne kan laifin hadin baki da yunkurin kisan kai da akayi a ranar 19 ga watan Yulin 2018 inda Melaye da 'yan dabarsa suka harbi Saja Danjuma Saliu a yayin da ya ke gudanar da aikinsa a hanyar Aiyetore Gbede, Mopa Road a jihar Kogi."

Mai magana da yawun 'yan sanda, Jimoh Moshood ya ce kotu ta basu izinin tsare Melaye har na tsawon kwanaki 14.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel