Daga Bauchi: Oshiomhole ya fallasa hanyoyin da Atiku ya ke samun kudaden kasuwancinsa

Daga Bauchi: Oshiomhole ya fallasa hanyoyin da Atiku ya ke samun kudaden kasuwancinsa

- Kwamred Adams Oshiomhole, ya yi zargin cewa Atiku Abubakar, ya samu kudaden da yake kasuwanci a yanzu, a lokacin da yake aiki a hukumar Kwastam

- Adams Oshiomhole, ya ce zai zama abun mamaki yadda Atiku yake kasuwanci da makudan kudade, wadanda kowa ya san ba zai taba samunsu daga albashinsa ba kawai

- Haka zalika ya ce zargin PDP na cewa APC na amfani da kudaden gwamnatin kasar wajen gudanar da yakin zabe karya ce tsagwaronta

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, ya yi zargin cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya samu kudaden da yake kasuwanci a yanzu, a lokacin da yake aiki a hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam).

Adams Oshiomhole, ya ce zai zama abun mamaki yadda Atiku yake kasuwanci da makudan kudade, wadanda kowa ya san ba zai taba samunsu daga albashinsa ba kawai, a hannu daya kuma shugaban APC na kasar, ya ce kudaden Atiku sun samune daga hanyar da bata dace ba.

Haka zalika ya yi zargin cewa jam'iyyar PDP da yan takararta na zargin cewa APC na amfani da kudaden gwamnatin kasar wajen gudanar da yakin zabe, yana mai bayyana hakan a matsayin karya tsagwaronta.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Shugaban kasa Buhari ya kaddamar da yakin zabensa a Bauchi

Daga Bauchi: Oshiomhole ya fallasa hanyoyin da Atiku ya ke samun kudaden kasuwancinsa

Daga Bauchi: Oshiomhole ya fallasa hanyoyin da Atiku ya ke samun kudaden kasuwancinsa
Source: Depositphotos

Oshiomhole yayi wannan jawabi ne a babban filin wasanni na Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi a ranar Asabar, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin zabensa, da kuma marabtar wasu jiga jigan jam'iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC.

Bayan soma taron, tare da gabatar da manyan baki, musamman shi uban taron, gwamnan jihar, Muhammadu Abdullahi Abubakar, mawaka sun baje kolinsu, inda Dauda Kahutu Rarara da su Jamila Nagudu, Naburuska, Baban Cinedu, Baba Ari da sauransu, suka nishadantar da mahalarta taron.

Wannan dai shine karo na hudu da shugaban kasar ya ziyarci jihar Bauchi, wanda gwamnan jihar ke kallo a matsayin nuna soyayyar shugaban kasar ga al'ummar jihar Bauchi. Haka zalika, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, shine ya tarbi wadanda suka sauya shekar cikin mutuntawa, da kuma mika tsintsiya garesu.

Da yake jawabi a madadin wadanda suka sauya sheka zuwa APC, Dr. Malam Isa Yuguda, ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gafarta masu kura kuran da suka aikata, musamman yadda gwamnatin PDP ta hana Buhari wajen da zai gudanar da yakin zabe a jihar, a 2015.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel