Da dumin sa: 'Yan sanda sun cafke wani gawurtaccen mai kera bindigogi a dajin Zamfara

Da dumin sa: 'Yan sanda sun cafke wani gawurtaccen mai kera bindigogi a dajin Zamfara

- Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara karkashin jagorancin CP, Zanna Muhammad Ibrahim ta samu nasar cafke wani sharararen makerin bindiga mai suna Umar Shehu.

- Kwamishinan ‘yansandar jihar ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zanta wa da manaima labarai a Hedikwatarsu da ke Gusau.

Kwamishinan ya bayyna cewa ‘Umar Shehu ya shahara wajen kera bindigogi kuma yana sai da wa jama’a. Don haka, wannna ya saba wa saboda haka zai fuskaci kuliya.

Da manema labarai suka tambayi Umar Shehu a kan kera bindogogi da ya ke yi ya shaida musu cewa, lallai shi ne yake kera su amma shi danbanga ne kuma mutanensu ‘yanbanga yake kera wa don su kare al’umma da su.

Da dumin sa: 'Yan sanda sun cafke wani gawurtaccen mai kera bindigogi a dajin Zamfara

Da dumin sa: 'Yan sanda sun cafke wani gawurtaccen mai kera bindigogi a dajin Zamfara
Source: Twitter

KU KARANTA: MTN da gwamnatin tarayya sun shirya tsakanin su

Ya ce, bai taba sai da wa wani ba, wanda ba danbanga ba. Y ace yana sai da kowace bindiga akan Naira dubu uku.

Kwamishina Zannah ya kuma bayyana nasara da suka samu na kwato wata mace daga hannu masu garkuwa da muta ne.

Kuma ya tabbata da cewa rundunar sa ba za ta lamuncin yin ta’addanci ba, musamman masu garkuwa da mutane da Mahara da kuma bata-gari, zaman lafiyar su shi ne su yi saranda su kaurace wa wadannan munanan ayyuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel