Da dumi dumi: Shugaban kasa Buhari ya kaddamar da yakin zabensa a Bauchi

Da dumi dumi: Shugaban kasa Buhari ya kaddamar da yakin zabensa a Bauchi

A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Bauchi, domin kaddamar da yakin zabensa a karo na biyu, shugaban kasar ya isa jihar, indai kai tsaye ya garzaya babban filin wasanni na Abubakar Tafawa Balewa da ke cikin kwaryar Bauchi, inda nan take, aka fara gudanar da shirye shiryen yakin zaben.

A wajen taron, akwai iiga jigan jam'iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, da suka hada da: Tsohon gwamnan jihar, Dr. Malam Isah Yuguda, tsohon gwamnan jihar, Dr Ahmad Muazu da sauransu, wadanda ake sa ran shugaban kasar zai marabce su a wajen taron.

Bayan soma taron, tare da gabatar da manyan baki, musamman shi uban taron, gwamnan jihar, Muhammadu Abdullahi Abubakar, mawaka sun baje kolinsu, inda Dauda Kahutu Rarara da su Jamila Nagudu, Naburuska, Baban Cinedu, Baba Ari da sauransu, suka nishadantar da mahalarta taron.

KARANTA WANNAN: Atiku ya juyawa Legas baya a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa - Tinubu

Yanzu yanzu: Shugaban kasa Buhari ya bar Abuja zuwa jihar Bauchi

Yanzu yanzu: Shugaban kasa Buhari ya bar Abuja zuwa jihar Bauchi
Source: Facebook

Wannan dai shine karo na hudu da shugaban kasar ya ziyarci jihar Bauchi, wanda gwamnan jihar ke kallo a matsayin nuna soyayyar shugaban kasar ga al'ummar jihar Bauchi. Haka zalika, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, shine ya tarbi wadanda suka sauya shekar cikin mutuntawa, da kuma mika tsintsiya garesu.

Da yake jawabi a madadin wadanda suka sauya sheka zuwa APC, Dr. Malam Isa Yuguda, ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gafarta masu kura kuran da suka aikata, musamman yadda gwamnatin PDP ta hana Buhari wajen da zai gudanar da yakin zabe a jihar, a 2015.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel