Atiku ya juyawa Legas baya a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa - Tinubu

Atiku ya juyawa Legas baya a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa - Tinubu

- Bola Tinubu, ya bayyana cewa Atiku Abubakar, ya juyawa jihar Legas baya a lokacin da aka tunkare shi kan wasu kudade da aka tauyewa jihar

- Tinubu ya yi ikirarin a mulkin Obasanjo, Atiku ya gaza yin komai lokacin da aka zabtare N250m daga kasafin kananan hukumomi na jihar

- Ooni na Ife, Oba Enitan Ogunwusi, ya sha alwashin cewa sarakunan zasu yi aiki tukuru wajen ganin cewa an gudanar da zabe ba tare da an samu hatsaniya ba

Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar APC na kasa kuma babban shugaban kungiyar yakin zaben jam'iyyar APC, ya bayyana cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya juyawa jihar Legas baya a lokacin da aka tunkare shi kan wasu kudade da aka tauyewa jihar a fannin samar da wutar lantarki, lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Oluseun Obasanjo.

Tinubu ya sanar da hakan a lokacin da ya karbi bakuncin sarakunan gargajiya na al'umar Yarabawa a Abuja, a ranar Juma'a.

Tinubu ya yi ikirarin cewa Atiku, wanda shine mataimakin shugaban kasa a lokacin, ya gaza yin komai lokacin da aka zabtare N250m daga kasafin jihar da ake aikawa, a lokacin da shi (Tinubu) yake gwamnan jihar Legas.

"Atiku ne mataimakin shugaba kasa, a lokacin da aka atuye kudin kananan hukumomin jihar Legas. Lokacin da muka kai kukanmu gaban Atiku a lokacin, sai yace mu tafi mu bashi waje, babu abunda zai iya yi mana.

KARANTA WANNAN: Ka daina yada labaran karya ko mu dauki mataki - Yan sanda sun gargadi Saraki

Atiku ya juyawa Legas baya a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa - Tinubu

Atiku ya juyawa Legas baya a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa - Tinubu
Source: UGC

"Sun kasance suna zabtare mana N250m a kasafin kudinmu na kowanne wata, kawai saboda sun fahimci muna da kirkira da kasuwanci. Duk inda muka juya, suna korarmu tare da azabtar damu. Amma bamu taba gajiyawa ba," a cewarsa.

Tinubu ya jinjinawa sarakunan gargajiyar bisa baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya, yana mai cewa: "Mun gode da kuka tsaya tsayin daka ba tare da juya baya ba. Mun gode da wannan ziyarar karfafa guiwar da kuka kawo mana. Ina cike da farinciki kuma ina alfahari da halin da yau muka tsinci kawunanmu a ciki. A lokacin da sarakuna suka amince da kai, to a lokacin ne ka san cewa jama'a na tare da kai, saboda muryar jama'a ita ce muryar ubangiji."

Ooni na Ife, Oba Enitan Ogunwusi, wanda ya jagoranci tawarar ya sha alwashin cewa sarakunan zasu yi aiki tukuru wajen ganin cewa an gudanar da zabe mai zuwa ba tare da an samu hatsaniya a cikin jama'a ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel