Ka daina yada labaran karya ko mu dauki mataki - Yan sanda sun gargadi Saraki

Ka daina yada labaran karya ko mu dauki mataki - Yan sanda sun gargadi Saraki

- Rundunar 'yan sanda ta zargi shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki da yada labaran karya, inda rundunar ta bukaci jama'a da su yi watsi da kalaman sa

- A wani taron manema labarai a Abuja, Saraki yayi zargin cewa akwai wasu 'yan ta'adda da ke aiki da jam'iyyar APC, sun kutsa gidan iyalansa da ke jihar Kwara

- Amma a wata sanarwa, Jimoh Moshood, kakakin rundunar 'yan sanda, ya ce Saraki bai wani shigar da karar farmakin ga rundunar 'yan sanda ba

Rundunar 'yan sanda ta zargi shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki da yada labaran karya, inda rundunar ta bukaci jama'a da su yi watsi da kalaman sa. Wannan ya biyo bayan wani ikirari da Saraki yayi na cewar rayuwarsa na cikin hatsari kuma rundunar 'yan sandan ta gaza bashi kariya.

A wani taron manema labarai a Abuja, Saraki yayi zargin cewa akwai wasu 'yan ta'adda da ke aiki da jam'iyyar APC, sun kutsa gidan iyalansa da ke jihar Kwara, inda suka lalata wasu kayayyaki da dama dake cikin gidan.

Ya ce akwai wasu 'yan sanda da suka baiwa wadanda ake zargin kariya, har zuwa lokacin da aka kammala aika-aikar.

KARANTA WANNAN: SGF: Tuni APC ta lashe zabe, kawai muna jiran INEC ta sanar da sakamako

Ka daina yada labaran karya ko mu dauki mataki - Yan sanda sun gargadi Saraki

Ka daina yada labaran karya ko mu dauki mataki - Yan sanda sun gargadi Saraki
Source: Depositphotos

Amma a wata sanarwa, Jimoh Moshood, kakakin rundunar 'yan sanda, ya karyata wannan zargi na Saraki. Ya ce shugaban majalisar dattijan bai wani shigar da karar farmakin ga rundunar 'yan sanda ba, har zuwa lokacin da ya gudanar da taron manema labarai.

Moshood ya ce rundunar ba zata kauce akan manunfofinta ba, kuma zata zamo mai taka tsan-tsan.

"Rundunar 'yan sanda bata baiwa wani dan bangar siyasa ko dan ta'adda da sunan APC kariya ba, a okacin da aka kai hari gidan iyalan shugaban majalisar dattijai, a Agbaji, Ilorin, inda aka lalata kayayyaki da shaguna da kuma yiwa mutane uku rauni da adduna, kamar yadda shi shugaban majalisar yayi ikirari," a cewar sa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel