Kamfen: Buhari zai kauracewa Kano saboda Ganduje

Kamfen: Buhari zai kauracewa Kano saboda Ganduje

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna shakku a kan ziyartar jihar Kano domin yakin neman zabe saboda rashin amsar da zai bawa Kanawa idan sun tambaye shi a kan faifan bidiyon zargin gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da karbar cin hanci.

Majiyar mu ta ce batun faifan bidiyon gwamna Ganduje na karbar cin hanci daga hannun wasu da ake zargin 'yan kwangila ne ya kara tasowa a wurin taron kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, lamarin da ya sa Buhari nuna kokonto a kan zuwa Kano kamfen.

A cikin shekarar da muka yi bankwana da ita ne wasu faifan bidiyo dake nuna gwamna Ganduje na karbar kudi da ake zargin cin hanci ne suka bayyana a kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta.

Kamfen: Buhari zai kauracewa Kano saboda Ganduje

Buhari da Ganduje
Source: Depositphotos

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewar ba lallai Buhari ya ziyarci Kano ba saboda badakalar da ake zargin Ganduje da ita.

An yi taron kwamitin ne domin tattauna hanyoyi da dabarun yakin kamfen din shugaba Buhari.

DUBA WANNAN: EFCC ta kama wani mutum da N75m a filin jirgin sama na Kano, hoto

Mamba a Kwamitin, Bashir Lado, ya nuna damuwarsa a kan jadawalin yakin neman zaben, yana mai bayar da shawarar cewar a saka jihohin Kano da Lagos a karshe saboda yawan jama'ar da suke da shi.

Da yake mayar da martani a kan kalaman Lado, Buhari ya tambaye shi "wacce amsa zan bawa mutanen Kano idan suka tambaye ni me yasa gwamnansu ke murmushi yayin karbar cin hanci?"

"Bani da amsar da zan basu. Ba zan iya zuwa Kano kamfen ba idan ba tilas hakan ya zama ba," Buhari ya fada ga yayin ganawar sirri da mambobin kwamitin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel