Gwamnatin Najeriya da kamfanin MTN sun sasanta kan su

Gwamnatin Najeriya da kamfanin MTN sun sasanta kan su

Gwamnatin Najeriya da kamfanin sadarwa na MTN sun cimma wata matsaya a wajen kotu kan takaddamar da su keyi kan fitar da wasu kudi da suka kai dalar amurka biliyan takwas daga kasar ba bisa ka'ida ba.

Gwamnatin kasar ta zargi kamfanin na kasar Afrika ta kudu ne da karya dokar hada-hadar kudaden ketare ta kasar.

Gwamnatin Najeriya da kamfanin MTN sun sasanta kan su

Gwamnatin Najeriya da kamfanin MTN sun sasanta kan su
Source: Twitter

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun tabbatar da harin su Shekau a Maiduguri

Legit.ng Hausa ta samu cewa bangarorin biyu dai basu bayyana yadda suka cimma matsayar ba, amma ga dukkan alamu wannan dambarwa ta jefa tsoro a zukatan sauran masu zuba jari a kasar.

Gwamnatin ta bukaci kamfanin na MTN da ya dawo da dala biliyan 8 da miliyan 100 zuwa asusun babban bankin kasar na CBN, haka zalika ta bukaci kamfanin da ya biya wasu dala biliyan 2 na daban a matsayin kudin haraji.

Sai dai kamfanin na MTN yaki yarda da cewa ya fitar da kudin ba bisa ka'ida ba, kuma kan haka ne ya shigar da karar gwamnatin kasar kan tarar da aka nemi ya biya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel