Yaki da rashawa: EFCC ta cika hannu da tsohon hadimin shugaba Goodluck Jonathan

Yaki da rashawa: EFCC ta cika hannu da tsohon hadimin shugaba Goodluck Jonathan

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin zagon kasa, EFCC, ta sake cika hannu da tsohon hadimin tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, Doyin Okupe, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Okupe, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP da kansa ya tabbatar da kamen da jami’an hukumar EFCC suka yi masa a ranar Juma’a 11 ga watan Janairu na shekarar 2019, inda yace hukumar ta bayyana masa cewa za ta makashi gaban kotu a ranar Litinin na mako mai zuwa.

KU KARANTA: An hana Atiku Abubakar dandalin gudanar da yakin neman zabe a yankin yarbawa

Yaki da rashawa: EFCC ta cika hannu da tsohon hadimin shugaba Goodluck Jonathan

Okupe
Source: Facebook

Itama hukumar EFCC ta tabbatar da kama Okupe, inda tace tana tuhumar Okupe ne da tafka laifukan da suka danganci karba da cin rashawa tare, inda tace a ranar Litinin 14 ga watan Janairu zata tasa keyarsa gaban babbar kotun tarayya na Abuja.

Sai dai Okupe ya bayyana cewa EFCC ta sauya ranar da aka yi zata shigar da shi gaban kotu ba tare da tuntubar lauyoyinsa ba, har sai a ranar Juma’a ne suka sanar da lauyoyinnasa.

Idan za’a tuna a watan Disambar shekarar data gabata ne jami’an hukumar EFCC suka yi ma gidansa dirar mikiya dake jahar Legas, inda suka bayyana masa wasu tuhume tuhume da suke dasu akansa, da suka hada da na satar kudi a shafukan yanar gizo.

Sai dai Okupe yace bayan sun bayyana masa manufar zuwansa gidannasa ne sai kuma suka nemi su tafi dashi, amma yaki amincewa saboda basu nuna masa wata shaida daga kotu data basu damar kamashi ba, inda yace sai dai ya bi su daga baya.

Amma jami’an hukumar sun tubure, har sai da suka tafi dashi, inda suka cigaba da rikeshi na tsawon kwanaki da dama suna yi masa tambayoyi tare da rubuta duk bayanan da yayi musu musamman game da lamurran da suka faru a lokacin dayake rike da mukamin siyasa a zamanin Goodluck.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel