Dino Melaye ya ki shiga asibtin DSS, ya kwanta a kasa

Dino Melaye ya ki shiga asibtin DSS, ya kwanta a kasa

Hayaniya sanata Dino Melaye da jami'an hukumar yan sanda bayan an daukeshi daga asibitin hukumar yan sanda zuwa asibitin hukumar leken asiri a DSS dake birnin tarayya Abuja.

Dan majalisan wanda ya kasance a hannun yan sanda tun makon da ya gabata da ya mika kansa ga hukumar ya ki shiga ginin hukumar DSS da akayi nufin shigar da shi domin yi masa jinya. A maimakon haka, ya kwanta a kasa

An tattaro cewa Sanatan ya tambaye jami'an tsaron shin ta wani dalili zasu kawoshi asibitin hukumar DSS. Da suka ki fada masa, ya lashi takobin ba zai shiga asibitin ba.

KU KARANTA: Shugaban yakin neman Atiku na yankin Arewa maso gabas ya koma APC

Dino Melaye ya ki shiga asibtin DSS, ya kwanta a kasa

Dino Melaye ya ki shiga asibtin DSS, ya kwanta a kasa
Source: UGC

Mun kawo muku rahoton cewa jami'an rundunar 'yan sandan Nigeria (NPF) ta sake cafke Dino Melaye, sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta Yamma a majalisar dattijai ta kasa.

A ranar Juma'ar nan rahotanni suka bayyana cewa wasu da ba a san ko su waye ba, sanye da hular da ta boye fuskarsu, suka kutsa cikin asibitin rundunar 'yan sanda dake Garki Abuja inda suka sace Melaye, wanda ke samun kulawar likitocin asibitin.

Yayinda hukumar yan sanda sukayi ikirarin cewa lafiyarsa kalau kuma zai iya gurfana a kotu, Sanata Dino Melaye ya jaddada cewa shi fa har yanzu bai da lafiya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel