Dalilin da yasa zan ba mata kaso 35 cikin 100 na mukamai a gwamnatina - Atiku

Dalilin da yasa zan ba mata kaso 35 cikin 100 na mukamai a gwamnatina - Atiku

- Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP), Atiku Abubakar ya bayyana cewa yawan adadin matan Najeriya da ke fitowa zabe a Najeriya shine yasa shi daukar alkawarin basu kaso 35 na mukamai a gwamnatinsa

- Atiku y ce a shekarun da yayi yana siyasa, mata na jajircewa wajen fitowa yin zabe sannan shima ya ci moriyar goyon baya daga gare su

- Bukola Saraki ya bayyana cewa mata za su taka muhimmiyar rawa a zaben Atiku Abubakar don ganin ya yi nasarar lashe zabe

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya bayyana cewa yawan adadin matan Najeriya da ke fitowa zabe a Najeriya shine yasa shi daukar alkawarin basu kaso 35 na mukamai a gwamnatinsa idan har aka zabe shi a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Abbakar a wajen taron matan PDP mai taken “Call for Action” da ya gudana a ranar Juma’a a Abuja yace shi baya tsoron mika mulkin kasar ga mata.

Dalilin da yasa zan ba mata kaso 35 cikin 100 na mukamai a gwamnatina - Atiku

Dalilin da yasa zan ba mata kaso 35 cikin 100 na mukamai a gwamnatina - Atiku
Source: Twitter

Ya yaba ma ata kan shirya wannan taro da suka yi, inda ya bayyana cewa a shekarun da yayi yana siyasa, mata na jajircewa wajen fitowa yin zabe sannan shima ya ci moriyar goyon baya daga gare su.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta kama dan Boko Haram din nan da ake nema ruwa a jallo (hoto)

A nashi bangaren, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa mata za su taka muhimmiyar rawa a zaben Atiku Abubakar don ganin ya yi nasarar lashe zaben da za a yi a watan Fabrairu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel