Shugaban yakin neman Atiku na yankin Arewa maso gabas ya koma APC

Shugaban yakin neman Atiku na yankin Arewa maso gabas ya koma APC

Shugaban yakin neman zaben dan takaran shugaban kasan jam'iyyar People’s Democratic Party PDP na yankin Arewa maso gabas, Sanata Saidu Umar Kumo. ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress, APC, game da cewar hadimin shugaban kasa.

Hadimin shugaban Buhari kan kafofin sada ra'ayi da zumunta, Bashir Ahmad, ya saki wata sako da ranan Juma'a, 11 ga watan Junairu, 2019 a shafinsa na Tuwita inda yace:

"Sanata Saidu Umar Kumo daga Gombe kuma shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku da PDP ya fita daga jam'iyyar PDP. Kana ya koma tafiyar "NextLevel".

A watan Junairu na shekaran 2018, Sanata Kumo ya fita daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Amma bayan watanni biyu kacal, ya sake komawa jam'iyyar PDP inda ya ce ya zama wajibi garesa ya koma domin taimakawa Atiku Abubakar wajen cin zaben 2019.

A watan Satumban da ya gabata, hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da shi kan almundahana da babakere.

KU KARANTA: Wani mutum ya sha da kyar a hannun fusatattun matasa

Mun kawo muku rahoton cewa kungiyar labaran sugaban kasa Buhari ta shawarci dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, da ya saduda domin guje ma shan kashi mafi kunya a zaben ranar 16 ga watan Fabrairun 2019.

Kungiyar BMO ta yi kiran ne a wani jawabi dauke das a hannun shugabanta, Mista Niyi Akinsiju, da sakatare, Mista Cassidy Madueke, a ranar Juma’a a Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel