Mohammed Bolori ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC

Mohammed Bolori ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC

Labari ya zo mana cewa Honarabul Mohammed Kaka Bolari ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki. Kaka Bolari yana cikin manyan jam’iyyar adawa ta PDP kafin wannan lokaci.

Mohammed Bolori ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC

Wani babban ‘dan siyasan Borno ya sauya sheka daga PDP
Source: Depositphotos

Hon. Mohammed Bolari wanda a da shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar a PDP ya bayyana cewa ba a taba samun lokacin da yankin Arewa maso Gabas ya amfana kamar a mulkin shugaba Buhari ba.

Kaka Bolari da mutanen sa sun ziyarci shugaban kasa Buhari a fadar Aso Villa domin tabbatar da mubaya’ar su ga gwamnatin APC mai-ci, inda ya tabbatarwa shugaban kasar cewa a da shi ne yake jagorantar yakin zaben PDP a Borno.

KU KARANTA: Wani Shugaban PDP a Jihar Kebbi ya dawo APC daf da zabe

Hon. Kaka Bolari ya zayyana irin kokarin gwamnatin APC a Arewa maso gabashin kasar nan, wanda su ka hada da tsarin N-Power, da sauran tsare-tsaren da su ka shafi rayuwar talakawan yankin, ban da kuma kokarin ganin bayan Boko Haram.

Babban ‘dan siyasar yana cikin wadanda PDP ta ke sa rai za su taya ta yakin neman zabe a 2019 a jihohin Adamawa, Gombe, Taraba, Bauchi. Borno da kuma jihar Yobe. Yanzu dai ya sha alwashin yi wa APC kamfe a zaben da za ayi a bana.

Dazu kun ji cewa wani shugaban jam’iyyar PDP mai adawa a jihar Kebbi ya sauya-sheka. Daily Trust ta rahoto cewa Mohammed Musa Bayawa Augie ya fice daga PDP ne ya koma jam’iyyar APC a makon nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel