Yanzu-yanzu: Tankan mai ya tashi da masu roron fetur

Yanzu-yanzu: Tankan mai ya tashi da masu roron fetur

Labarin da ke shigo mana da dumi-dumi na nuna cewa wata tankar man fetur ta kama da wuta a Odukpani, jihar Cross River. Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane ashirin masu roron man fetur biyar sun rasa rayukansu zuwan yanzu da muke kawo rahoto.

Tankar mai dauke da man fetur ta fadi ne a hanyar Ikom-Kalaba kusa da Federal Housing estate.

Wani idon shaida yace da yiwuwan mutanen da suka rasa rayukansu sun fi hakan yawa saboda har yanzu wuta na ci bal-bal

Idon shaidan ya kara da cewa ya ga mutane sun zuwa roron mai da galoli domin diban mai lokacin tankar ta fadi. Da wutan ya kama, basu samu daman gujewa ba.

Ku saurari cikakken rahoton..

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel