An hana Atiku Abubakar dandalin gudanar da yakin neman zabe a yankin yarbawa

An hana Atiku Abubakar dandalin gudanar da yakin neman zabe a yankin yarbawa

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP ta soki lamirin gwamnatin jahar Ekiti na haramta ma dan takararta, Atiku ABubakar amfani da babban filin wasanni na jahar dake garin Ado Ekiti wajen gudanar da gangamin yakin neman zabe.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kwamitin yakin neman zaben ta nemi gwamnatin jahar ta bata filin wasanni na Oluyemi Kayode don ta tara ma Atiku Abubakar jama’a a kokarinta na tallatashi tare da cika masa burinsa na zama shugaban kasar Najeriya.

KU KARANTA: Buhari ya mika ta’aziyyarsa bisa rasuwar wani babban basarake daga yankin Arewa

Haka zalika jam’iyyar ta zargi gwamnatin jahar Ekiti a karkashin Gwamna Kayode Fayemi na jam’iyyar APC da tura yan sara suka zuwa tsohon gareji dake unguwan Ijoka inda suka kai ma yan kasuwa masu tallace tallace hari.

Babban daraktan yakin neman zaben, Dipo Anisoluwa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhami, 10, ga watan Janairu, a garin Ado Ekiti inda yace gwamnatin jam’iyyar APC ta jahar Ekiti tana matsa ma abokan hamayya.

“Abinda ya fi muhimmanci ga dan takararmu Atiku Abubakar shine ya gana da jama’an jahar Ekiti, kuma muna sa ran zamu tara masa jama’a koda gwamnatin jahar Ekiti ta bami filin ko ta hanamu. Tarihi zai tuna da gwamnatin tsohon Gwamna Ayodele Fayose a lokacin daya baiwa Buhari dandalin inda ya shirya gangaminsa.” Inji shi.

Sai dai gwamnatin jahar Ekiti ta musanta zargin da jam’iyyar PDP ta yi mata na hanata amfani da filin wasan, kamar yadda kaakakin gwmanan jahar, Olayinka Oyebode ya bayyana, inda yace ana gudanar da aikin kwaskwarima ne a filin, don haka bai kamata ayi amfani da filin ba a yanzu.

Kaakakin yace sun baiwa PDP wani dandali na daban wanda aka ginashi musamman don shirya tarukan siyasa, inda yace hatta bikin nadin Gwamna Fayemi ma a dandalin aka shiryashi, haka zalika APC zata gudanar da gangaminta a dandalin, gangamin da ake sa ran mataimakin shugaban kasa Osinbajo zai halarta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel