Kungiyar kamfen din Buhari ta shawarci Atiku da ya dauki hakuri kawai

Kungiyar kamfen din Buhari ta shawarci Atiku da ya dauki hakuri kawai

- Kungiyar labaran sugaban kasa Buhari ta shawarci dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da ya saduda domin guje ma jin kunya 2019

- Kungiyar ta bayar da wannan shawarar don mayar da martani ga sauya shekar manyan yan PDP hudu zuwa jam’iyyar APC

- Mataimakin shugaban PDP (Arewa) Sanata Babayo Gamawa na daga cikin manyan jam’iyya da suka sauya sheka zuwa APC

Kungiyar labaran sugaban kasa Buhari ta shawarci dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, da ya saduda domin guje ma shan kashi mafi kunya a zaben ranar 16 ga watan Fabrairun 2019.

Kungiyar BMO ta yi kiran ne a wani jawabi dauke das a hannun shugabanta, Mista Niyi Akinsiju, da sakatare, Mista Cassidy Madueke, a ranar Juma’a a Abuja.

Kungiyar kamfen din Buhari sun sawarci Atiku da ya dauki hakuri kawai

Kungiyar kamfen din Buhari sun sawarci Atiku da ya dauki hakuri kawai
Source: Depositphotos

Jawabin yace kungiyar ta bayar da wannan shawarar don mayar da martani ga sauya shekar manyan yan PDP hudu a jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kungiyar tace ta bayar da shawarar ne bisa ga yadda Atiku da PDP ke rasa manyan mambobin jam’iyyar ga APC a kullun.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar alakar da ke tsakanin Amina Zakari da Buhari, dalilin da yasa akwai bukatr cire ta Ezekwesili

Kamfanin dillancin Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa mataimakin shugaban PDP (Arewa) Sanata Babayo Gamawa na daga cikin manyan jam’iyya da suka sauya sheka zuwa APC.

Kungiyar ta bayyana cewa sauya shekar babba ne.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel