Shugaban rundunar 'yan sanda na neman ya halaka ni - Saraki

Shugaban rundunar 'yan sanda na neman ya halaka ni - Saraki

- Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi ikirarin cewa Sufeta Janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris yana son ya kashe shi

- Shugaban majalisar ya ce 'yan sandan sun dade suna yunkurin jefa rayuwarsa cikin hatsari

- Saraki ya yi kira da hukumomin kasashen waje su kama Idris idan wani abu ya same shi ko iyalansa

A yau, Juma'a 11 ga watan Janairu ne shugaban majalisar dattawar Najeriya, Bukola Saraki ya koka cewa shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris yana barazana ga rayuwarsa kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Shugaban rundunar 'yan sanda na neman ya halaka ni - Saraki

Shugaban rundunar 'yan sanda na neman ya halaka ni - Saraki
Source: Twitter

Legit.ng ta gano cewar, Saraki wadda shine direktan yakin neman zaben dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019 ya yi kira ga hukumomin kasashen waje su damke Idris idan wani abu ya faru dashi ko iyalansa.

DUBA WANNAN: Jihohi 10 da suka fi bunkasa a Najeriya a yanzu

Ya ce, "IGP ya yi amfani da dabaru daban-daban domin ya kama shi da laifi, da farko ya kama wasu 'yan kungiyar asiri kuma ya tilasta musu cewa suna yi masa aiki ne.

"Daga bisani, ya yi amfani da fashin bankin Offa inda ya yi kokarin jefa suna na a ciki. A yunkurinsa na tilastawa wanda ake zargi da fashin ya ambaci suna na ya mutu a hannunsu. Bai yi nasara ba ma a nan. Wanne ya san abinda ya ke shiryawa kuma?

Shugaban majalisar ya ce, "Ya kamata su sanar da duniya yanzu da zamu fara kamfen daga mazaba zuwa mazaba kamar yadda muka saba yi idan lokacin zabe ya karato.

"Babu wanda ya san irin umurninda Mr Idris ya bawa 'yan sandan jihohi.

"Saboda haka, duniya ta damke Sufeta Janar na 'yan sanda idan wani abu ya faru da iyalai na ko ni kai na."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel