Rundunar soji ta kama dan Boko Haram din nan da ake nema ruwa a jallo (hoto)

Rundunar soji ta kama dan Boko Haram din nan da ake nema ruwa a jallo (hoto)

- An kama wani dan ta’addan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo

- An gano Dan ta'addan mai suna Babagana Abubakar (wanda aka fi sani da Alagarno) a garin Bulabulim Ngarnam

- Tare da shi akwai wasu kayayyaki da suka hada da na sojoji, katunan zabe da sauransu

Rundunar soji ta kama wani dan ta’addan Boko Haram mai suna Babagana Abubakar (wanda aka fi sani da Alagarno) da ake nema ruwa a jallo a garin Bulabulim Ngarnam da ke wajen garin Maiduguri.

An bayyana akan ne a wani jawabi da aka saki a ranar Alhamis, 10 ga watan Janairu daga hannun Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman, darakta janar na labaran rundunar.

Legit.ng ta tattaro cewa rundunar hadin gwiwa ta Bataliya 195 da jam ian yan sanda da kuma yan bangan CJTF ne suka kama shi.

Rundunar soji ta kama dan Boko Haram din nan da ake nema ruwa a jallo (hoto)

Rundunar soji ta kama dan Boko Haram din nan da ake nema ruwa a jallo
Source: UGC

Jawabin ya zo kamar haka: “Dakarun sojin sashi 7 da ke gudanar da ayyuka bincike tare da hadin gwiwar rundunar Bataliya 195, jami’an yan sanda da yan CJTF, a wasu yankunan Maiduguri a yau sun gano tare da kama wannan shahararren dan ta’addan Boko Haram da ake kira da Babagana Abubakar (aka Alagarno), inda yake boye a garin Bulabulim Ngarnam.

KU KARANA KUMA: Gaskiyar alakar da ke tsakanin Amina Zakari da Buhari, dalilin da yasa akwai bukatr cire ta Ezekwesili

“An gano shi boye a wani daki dauke da kayan sojoji biyu, akalmin soji daya, da wani riga da ake daurawa a saman kaya, kayan yan kwallo, gajeren wando na sojoji, katunan zabe biyu, da katin shaidar zama dan kansa, rigar sojoji, da hular sojoji. Tuni an mayar da shi sashin amsa tambayoyi."

A baya Legit.ng ta tattaro cewa sashin kwararru Inspekto Janar na yan sanda sun kama wani dan ta’addan Boko Haram mai suna Umar a Lagas.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel