Kungiyar hadin gwiwar jam'iyyu ta kalubalanci Buhari kan jagorantar yakin neman zaben sa

Kungiyar hadin gwiwar jam'iyyu ta kalubalanci Buhari kan jagorantar yakin neman zaben sa

- Kungiyar hadin gwiwar jam'iyyu ta ce Buhari ya jagoranci yakin neman zaben sa da kansa

- CUPP ta nemi shugaba Buhari ya tabbatar da cancantarsa da dacewa ta jagorancin Najeriya

- Ta kuma zargi shugaba Buhari da kulla kutungwila ta magudi a zaben 2019

Kungiyar hadin kan jam'iyyu ta Coalition of United Political Parties, CUPP, ta kirayi shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan ya karbi ragamar jagorancin yakin neman zaben sa domin ya tabbatar da cancantar sa ta jagorantar Najeriya.

CUPP ta kirayi shugaba Buhari da ya karbe ragamar jagorancin kungiyar yakin neman zaben sa daga hannun kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, domin ya tabbatar da cancantar sa da kuma dacewarsa ta jagorancin kasar nan.

Kungiyar ta kuma zargi jam'iyya mai mulki ta APC da kulla kutungwila ta shirin aiwatar da magudi a yayin babban zaben kasa da hakan ka iya jefa kasar nan cikin rudani da kuma tarzoma kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Kungiyar hadin gwiwar jam'iyyu ta kalubalanci Buhari kan jagorantar yakin neman zaben sa

Kungiyar hadin gwiwar jam'iyyu ta kalubalanci Buhari kan jagorantar yakin neman zaben sa
Source: Facebook

Yayin gabatar da jawabansa ga manema labarai cikin birnin Abuja a yau Juma'a, shugaban kungiyar, Olagunsoye Oyinlola, ya ce Buhari zai kasance shugaban kasa na farko a tarihin Najeriya da zai dauki hayar wani domin jagorantar yakin neman zaben sa.

Kungiyar da ta kunshi fiye da jam'iyyu 46 na Najeriya, ta ce dole shugaba Buhari ya yi muhawara a tsakanin sa da sauran 'yan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyu domin zayyanawa al'ummar Najeriya irin rikon sakainar kashi da ya yiwa akalar su ta jagoranci.

KARANTA KUMA: An gudanar da jana'izar Sarkin Lafiya, Isa Agwai

Jagoran kungiyar ya kuma bayyana cewa, gazawar shugaba Buhari da hawan sa bisa kujerar naki a kan kudirin gyara dokar zabe wata kitimurmura ce ta cin karen sa ba bu babbaka a zaben kasa da ke matukar barazana ga nagartar hukumar zabe.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya zargi shugaban kasa Buhari da jam'iyyar APC da sabawa dokar zabe ta kasa wajen amfani da dukiyar baitul mali a yakin su na neman zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel