Mun mayar da Melaye asibitin hukumar DSS - Rundunar 'yan sanda ta yi karin haske

Mun mayar da Melaye asibitin hukumar DSS - Rundunar 'yan sanda ta yi karin haske

Rundunar 'yan sanda ta ce ta mayar da sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye zuwa asibitin sashen hukumar tsaron cikin gida DSS da ke Abuja. Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Mr Jimoh Moshood, ya tabbatar da hakan a zantawarsa da gidan talabijin na Channels.

Mr Moshood ya bayyana cewa an dauke dan majalisar daga asibitin rundunar 'yan sanda dake Garki, Abuja, zuwa asibitin hukumar tsaro ta DSS, bayan da sanatan da 'yan sandan suka yi takaddama akan lafiyarsa, domin fara binciken zargin da ake yi masa.

Moshood ya kara bayyana cewa rundunar yan sanda ta samu waranti na ci gaba da tsare sanatan a wajenta, wanda warantin ya fara aiki daga ranar 9 ga watan Janairu, kuma zai shafe kwanaki 14 a tsare.

KARANTA WANNAN: Yadda APC ta bani cin hanci don barin PDP amma naki yarda - Tambuwal

Yanzu yanzu: Rundunar 'yan sanda ta sake cafke Dino Melaye a karo na biyu

Yanzu yanzu: Rundunar 'yan sanda ta sake cafke Dino Melaye a karo na biyu
Source: UGC

A nasu bangaren, iyalan Sanata Melaye sun koka kan yadda ake kuntatawa dan majalisar bayan da aka dauke shi daga asibitin yan sanda zuwa na hukumar DSS. Sun ce har yanzu ba a sanar da su dalilin canja masa asibiti ba.

Mani makusancin Sanata Melaye, ya shaidawa Channels TV cewar an kai ruwa rana a lokacin da aka yi yunkurin kaishi asibitin hukumar DSS, inda shi Sanatan yaki amincewa da wannan canji.

Duk da cewa, rundunar 'yan sanda ta jaddada cewa dan majalisar ya samu lafiyar da zai iya fuskantar bincike da tuhuma, akan zargin da ake masa na harbin wani jami'in dan sanda, Melaye ya ce yana bukatar lokaci don murmurewa.

Rundunar 'yan sanda dai bata bayar da wata sanarwa kan wannan rahoto ba, har zuwa lokacin da aka kammala rubuta wannan labari.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel