Manyan Jam’iyyar PDP sun shiryawa Tinubu makarkashiya – kungiyar APC

Manyan Jam’iyyar PDP sun shiryawa Tinubu makarkashiya – kungiyar APC

Wata kungiya da ke tare da jam’iyyar APC mai mulki ta nemi jami’an tsaro su kara zage dantse wajen ganin an ba babban jigon jam’iyyar da wasu kusoshi a APC kariya a lokacin da ake shirin zabe.

Manyan Jam’iyyar PDP sun shiryawa Tinubu makarkashiya – kungiyar APC

Wasu 'yan kungiyar APC sun yi kira a kara kare Bola Tinubu
Source: Depositphotos

Kungiyar ta ‘Broom Revolution’ ta nemi jami’an tsaro Najeriya su karawa Bola Ahmed Tinubu da wasu jagororin jam’iyyar tsaro. Shugaban kungiyar na kasa baki daya watau Mohammed Abubakar shi ne yayi wannan jawabi.

Mohammed Abubakar yayi wannan kira ne a garin Lokoja a cikin jihar Kogi a wata zantawa da yayi da ‘yan jarida na kasar. Abubakar ya zargi jam’iyyar adawa na PDP da shirya makarkashiya a babban zaben da za ayi a 2019.

KU KARANTA: Wata kungiya ta sha alwashin kawowa Atiku kuri’u miliyan 5

Shugaban kungiyar na Broom Revolution yace wasu jagororin PDP su na da shirin shigo da wasu kayan aiki daga kasar waje. Mohammed Abubakar yayi amfani da wannan dama ya maidawa Timi Frank martani a kan kalaman sa.

Timi Frank, wanda yana cikin manyan APC a baya, ya zargi jam’iyyar APC da gwamnatin ta da shirin ganin bayan manyan ‘yan jam’iyyar adawa na kasar. Mohammed Abubakar yace babu kanshin gaskiya abin da Frank ya fada.

Yanzu haka dai Asiwaju Bola Tinubu ne jagoran yakin zaben shugaba Muhammadu Buhari. Shugaban kasar ya sallama masa komai game da kamfe don haka kungiyar ta Broom Revolution ta nemi jami’an tsaro su kara masa kariya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel