Gaskiyar alakar da ke tsakanin Amina Zakari da Buhari, dalilin da yasa akwai bukatr cire ta Ezekwesili

Gaskiyar alakar da ke tsakanin Amina Zakari da Buhari, dalilin da yasa akwai bukatr cire ta Ezekwesili

- Yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar ACPM, Oby Ezekwesili, ta yi kira ga a tsige Amina Zakari a matsayin shugabar kwamitin fadar sakamako na hukumar INEC

- Ezekwesili tace, don kare mutunci, kada a bari Amina ta gudanar da kowani aiki a lokaci da bayan zabe

- Ta ta bayyana ikirarin fadar shugaban kasa da INEC na cewa babu alakar jini tsakanin shugaba Buhari da Amina Zakari a matsayin karya, inda ta kara da cewa akwai alaka ta aure

Oby Ezekwesili, yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar Allied Congress Party of Nigeria (ACPM), ta yi kira ga a tsige Amina Zakari daga matsayin shugabar kwamitin fadar sakamako na hukumar zabe mai zaman kanta.

A cewar Ezekwesili, don kare mutunci, kada a bari Amina ta gudanar da kowani aiki a lokaci da bayan zabe, Channels TV ta ruwaito.

Yar takarar shugabar kasa a jam’iyyar ta ACPM ta bayyana ikirarin fadar shugaban kasa da INEC na cewa babu alakar jini tsakanin shugaba Buhari da Amina Zakari a matsayin karya, inda ta kara da cewa akwai alaka ta aure.

Gaskiyar alakar da ke tsakanin Amina Zakari da Buhari, dalilin da yasa akwai bukatr cire ta Ezekwesili

Gaskiyar alakar da ke tsakanin Amina Zakari da Buhari, dalilin da yasa akwai bukatr cire ta Ezekwesili
Source: UGC

Ezekwasili tace: “Abun kunya ne cewa suna karya. Sun san cewa yar’uwar shugaban kasar na auren mahaifin Amina Zakari. Hakan ya nuna akwai alaka mai karfi. Bana daga cikin jam’iyyar da ta yi Magana game da alaka ta jini.

KU KARANTA KUMA: Anzo wajen: Dino Melaye ya samu lafiya, zai iya fuskantar shari'a yanzu - Asibitin 'yan sanda

“Na san cewa babu nasaba ta jini, amma na san cewa akwai kusanci sosai a tsakaninsu. Kuma alakarsu abune da ake nunawa a ko ina ar sa yanzu da ya zama matsala."

A baya mun ji cewa dangin babbar jami’ar hukumar zaben nan na kasa na INEC watau Amina Zakari wanda har gobe ake ce-ce-ku-ce a game da sabon mukamin da aka ba ta sun fito sun yi magana game da surutun da ake yi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel