Kishi: Wani miji ya kashe saurayin tsohuwar matarsa bayan ya gansu a daki tare

Kishi: Wani miji ya kashe saurayin tsohuwar matarsa bayan ya gansu a daki tare

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Benue ta gurfanar da wai Abunde Goja mai shekaru 32 a gaban kuliya bisa zarginsa da kashe saurayin tsohuwar matarsa.

Wanda ake zargin ya kaiwa saurayin tsohuwar matarsa hari ne bayan ya tarar da su tare a cikin wani daki a gidan mahaifinta.

Ana tuhumar Goja da laifin hadin baki, kisar gilla da kuma kasancewa mamban wata haramtaciyar kungiya a gaban alkalin babban kotun Makurdi.

'Yar sanda mai shigar da kara, Inspecta Veronica Shaagee ta ce Goja antayawa Mr Terdoo Shitov acid sannan shi da abokansa suka rika sarar sa da adda.

Kishi: Wani miji ya kashe saurayin tsohuwar matarsa bayan ya gansu a daki tare

Kishi: Wani miji ya kashe saurayin tsohuwar matarsa bayan ya gansu a daki tare
Source: Twitter

Ta ce ya kashe Mr Shitov ne a gidan mahaifin tsohuwar matarsa da ke Judges Quarters a Makurdi.

Ta shaidawa kotu cewa an mika binciken laifi daga caji ofis din 'yan sanda na B division da ke Makurdi zuwa sashin binciken manyan laifu wato CIID a ranar 7 ga watan Janairun 2019.

DUBA WANNAN: Jihohi 10 da suka fi bunkasa a Najeriya a yanzu

"A yayin da tsohuwar matar Goja ta ke zaune da saurayinta Terdoo Shitov a gidan mahaifinta, tsohon mijinta Bunde Goja tare da abokansa 'yan kungiyar asiri suka shigo suka fara sarar Shitov da adduna kuma suka antaya masa acid a kai."

'Yar sanda mai shigar da karar ta ce wanda ake tuhuma ya amsa cewa shine ya aikata laifin a yayin da ake masa tambayoyi.

Ta ce an gano addar da jini, katako, gatari da robar acid da tufafe da jini a jiki a wurin da aka aikata laifin.

Shaagee ta ce har yanzu ba a kammala bincike ba kuma ta bukaci kotu ta dage sauraron shari'ar har zuwa lokacin da aka kammala binciken.

Ta ce laifukan sun sabawa sashi na 97, 222 na Penal Code na jihar Benue da kuma sashi na 11(2) hana sata da garkuwa da mutane da shiga kungiyoyin asiri na 2017.

Alkalin kotun, Mrs Fatima Akintomide ta bayar da umurnin a cigaba da tsare Goja a gidan yari sannan ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Fabrairun 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel