Wata kungiya ta amince da Atiku, ta sha alwashin kawo masa kuri’u miliyan 5

Wata kungiya ta amince da Atiku, ta sha alwashin kawo masa kuri’u miliyan 5

- Wata kungiyar yan ta kaddamar da goyon bayanta gad an takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a zabe mai zuwa

- Kungiyar tayi bayanin cewa kungiyar ta kaddamar da Atiku a matsayin dan takararta saboda shine yafi cancanta da wannan tseren

- Ta kuma jadadda cewa za ta kawo wa Atiku kuri’u miliyan biyar daga yankin kudu maso gabas a zabe mai zuwa

Wata kungiyar yan Igbo mai suna Igbo Mandate for Good Governance, ta kaddamar da goyon bayanta gad an takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar a zabe mai zuwa.

Shugaban kungiyar na kasa, Mista Sabinus Amako, ya bayyana matsayar kungiyar ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a Owerri a ranar Juma’a, 11 ga watan Janairu.

Amako yayi bayanin cewa kungiyar ta kaddamar da Atiku a matsayin dan takararta saboda shine yafi cancanta da wannan tseren.

Wata kungiya ta amince da Atiku, ta sha alwashin kawo masa kuri’u miliyan 5

Wata kungiya ta amince da Atiku, ta sha alwashin kawo masa kuri’u miliyan 5
Source: Twitter

Ya bayyana tsohon mataimakin shugaban kasar a matsayin aiken Allah, inda ya kara da cewa Atiku da Obi ne za su iya daidaita tattalin arzikin kasar.

A cewar kungiyar shugabancin Atiku da Obi zai samar da hanyoyin kasuwanci da kuma dawo da mutunta doka.

Ya kuma jadadda cewa kungiyar za ta kawo wa Atiku kuri’u miliyan biyar daga yankin kudu maso gabas a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Buhari bai da ilimin tattalin arziki – Titi Abubakar

Ya bukaci mambobin kungiyar da su tabbatar sun karbi katunan zabeensu domin shirya ma zaben.

A cewarsa cikin dukkanin masu neman takarar wannan kujera ta shugabancin ksar, Atiku ne kadai ya cancanci rike mukamin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel