An karrama Tinubu da Balarabe Musa da lambobin yabo

An karrama Tinubu da Balarabe Musa da lambobin yabo

Gidauniyar Arewa ta karrama wasu fitattun 'yan Najeriya da suka nuna bajinta da jarumta a fagen ayyukansu, cikin wadanda aka karramar har da jagoran APC na kasa, Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa da wasu fittatun 'yan Najeriya.

Jagoran jam'iyyar All Progressive Congress APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Balarabe Musa suna daga cikin wadanda suka samu lambar yabo daga gidauniyar Arewa (Arewa Foundation).

A liyafar girmamawa karo na farko da gidauniyar ta shirya a Legas, an karrama Tinubu da lambar yabo na Sardauna Award for Leadership; shi kuma Balarabe Musa an karrama shi da lambar yabo na Aminu Kano saboda hidima da ya ke yiwa al'umma.

An karrama Tinubu da Balarabe Musa da lambobin yabo

An karrama Tinubu da Balarabe Musa da lambobin yabo
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Jihohi 10 da suka fi bunkasa a Najeriya a yanzu

Sauran wadanda aka karrama a wurin taron sun hada da Direkta-Janar na Cibiyar Zanen motocci da habbaka su wato Nigerian Automotive Design and Development Concil, Aliyu Jelani inda ya lashe lambar yabo na Arewa Entrepreneur of the Year.

Kazalika, Hadiza Bala, Shugaban Hukumar Kulawa da Tashohin Jiragen Ruwa na Najeriya itama tana cikin wadanda aka karrama da lambar yabon kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gidauniyar tana mayar da hankali ne kan 'yan Najeriya da suka bayar da gudunmawa a ayyukansu mabanbanta domin kara musu kwarin gwiwa da kuma amfani da su a matsayin misali ga takwarorinsu da kuma matasa da ke tasowa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel