APC aljannar barayin yan siyasa ce – Tambuwal

APC aljannar barayin yan siyasa ce – Tambuwal

- Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin aljannar barayin yan siyasa

- Yace jam’iyyar na boye duk wani da ke da guntun kashi a tsuliyarsa muddin zai koma cikinta

- Tambuwal ya roki dukkanin jama’a da su zabi PDP a zabe mai zuwa idan har suna so su kore duk wani wahalhalu da matsin rayuwa, rashin tsaro da kuma gurbatacciyar shugabanci da ake ciki a yanzu

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) kamar yadda take a yau ba komai bace face aljanna ga wadanda ke da guntun kashi a tsuliyarsu.

Tambuwal wanda yayi wannan hasashen a taron magoya bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Wurno a jiya ya gargadi yan Najeriya akan ci gaba da sauraron karairayi daga APC.

A cewar shi, yan Najeriya sun ga yadda kasar ta zama a cikin shekaru hudu da suka gabata a gwamnatin APC.

APC aljannar barayin yan siyasa ne – Tambuwal

APC aljannar barayin yan siyasa ne – Tambuwal
Source: Depositphotos

Gwamnan ya roki dukkanin jama’a da su zabi PDP a zabe mai zuwa idan har suna so su kore duk wani wahalhalu da matsin rayuwa, rashin tsaro da kuma gurbatacciyar shugabanci da ake ciki a yanzu.

Gwamnan ya ci gaba da bayyana APC a matsayin kungiyar mutane mayaudara, don haka akwai bukatar a daina yarda da karairayin da ke fita daga bakunansu.

KU KARANTA KUMA: Tsohon shugaban matasan PDP da wasu 157 sun sauya sheka zuwa APC a Abaji

A wani lamari na daban, mun ji cewa Sanata Sani ya gargadi wani tsohon shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa aka shirinsa na sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Alamu sun nuna cewa tsohon shugaban PDP na yunkurin komawa jam’iyyar APC a lokacin gangamin jam’iyyar na arewa maso gabas da aka shirya gudanarwa a Bauchi a karshen mako.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel