Rundunar 'yan sanda ta bukaci gwajin jinin Cristiano Ronaldo kan zargin fyade

Rundunar 'yan sanda ta bukaci gwajin jinin Cristiano Ronaldo kan zargin fyade

- Rundunar 'yan sanda ta Las Vegas ta bukaci shahararren dan wasan kwallon kafar nan Cristiano Ronaldo da ya gabatar mata da gwajin jinisa

- Bukatar gwajin jinin nasa ya biyo bayan wani zargi da ake yi masa na yiwa wata tsohuwar mai tallace tallace fyade a shekarar 2009

- Kathryn Mayorga tayi ikirarin cewa Ronaldo ya yi mata fyade a dakinsa da ya kama a wani otel a ranar 13 ga watan Yuni 2009, kafin ya fara buga wasa a Real Madrid

Rundunar 'yan sanda ta Las Vegas ta bukaci shahararren dan wasan kwallon kafar nan Cristiano Ronaldo da ya gabatar mata da gwajin jinisa, a cikin binciken da take gan gudanarwa na zargin da ake yi masa na aikata laifin fyade.

Dan wasan gaban Juventus ya karyata wannan zargi da ake yi masa, ta bakin lauyansa, Peter Christiansen, inda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, cewar wannan bukatar na da tsauri.

"Mr Ronaldo na da taka tsantsan a kullum, kamar yadda yayi a yanzu, abun da ya faru a Las Vegas a 2009 wani lamarine na kaddarar rayuwa, don haka ba zai zama abun mamaki don an bukaci gwajin jininsa ba, amma bamu yi tunanin cewa rundunar 'yan sandan zata gabatar da wannan bukatar a yanzu ba," ya ce a cikin wata sanarwa.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Rundunar 'yan sanda ta sake cafke Dino Melaye a karo na biyu

Rundunar 'yan sanda ta bukaci gwajin jinin Cristiano Ronaldo kan zargin fyade

Rundunar 'yan sanda ta bukaci gwajin jinin Cristiano Ronaldo kan zargin fyade
Source: Twitter

Rundunar 'yan sanda ta Las Vegas ta ce ta gabatar da wannan bukatar ne ga hukumomin Italia, inda ta kara da cewa "daukar wannan matakin ba wai a kansa kadai bane, ya dogara ne akan duk wani da ake zarginsa da yin fyade, dole ne a bukaci gwajin jininsa."

Tsohuwar yar tallace tallace, Kathryn Mayorga, mai shekaru 34, da ke da zama a Las Vegas, ta zargi Ronalad da yi mata fyade, a wani korafi da ta shigar karshen shekarar data gabata a garin Nevada.

Ta yi ikirarin cewa bayan haduwarta da shi a wani dakin rawar dare a Las Vegas, ya yi mata fyade a dakinsa da ya kama a wani otel a ranar 13 ga watan Yuni 2009, kafin ya fara buga wasa a Real Madrid, bayan barinsa Manchester United.

Mayorga ta yi ikirarin cewa an biyata $375,000 domin ta yi shiru da bakinta kan wannan lamari.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel