Shehu Sani ya gargadi tsohon shugaban PDP na kasa akan yunkurin komawa APC

Shehu Sani ya gargadi tsohon shugaban PDP na kasa akan yunkurin komawa APC

- Jam’iyyar APC na shirin tarban tsohon shugaban PDP, Alhaji Adamu Mu’azu zuwa inuwarta

- Ana sanya ran Mu’azu zai koma APC a lokacin gangamin jam’iyyar na arewa maso gabas

- Sanata Shehu Sani ya gargadi Mu’azu akan yunkurin siyasarsa na gaba

Sanata Sani ya gargadi wani tsohon shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa aka shirinsa na sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Alamu sun nuna cewa tsohon shugaban PDP na yunkurin komawa jam’iyyar APC a lokacin gangamin jam’iyyar na arewa maso gabas da aka shirya gudanarwa a Bauchi a karshen mako.

Mu’azu, tsohon gwamnan jihar Bauchi na wajen kasar Najeriya sama da shekaru uku har sai watan Disamba 2018 lokacin da ya dawo kasar sannan ya aurar da yarsa.

Shehu Sani ya gargadi tsohon shugaban PDP na kasa akan yunkurin komawa APC

Shehu Sani ya gargadi tsohon shugaban PDP na kasa akan yunkurin komawa APC
Source: Facebook

Bikin auran ya samu halartan matamakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da manyan shugabannin APC ciki harda gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar.

Daga nan, sai Mu’azu ya ziyarci Osinbajo a fadar shugaban kasa a ranar Laraba, b19 ga watan Disamba amma yaki Magana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawar da suka kwashi sama da sa’o’i biyu.

KU KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Ali Nuhu ya cika Shekaru 20 a masana’antar shirya fina-finan Hausa

Sanata Sani ya je shafin twitter a ranar Alhamis, 10 ga watan Janairu ida yayi amfani da karin magana wajen gargadin Mu’azu akan yunkurin siyasarsa na gaba.

A wan lamari makamancin haka mun ji cewa tsohon shugaban matasa na babbar jam’iyyar adawa Peoples Democratic Party (PDP) a mazabar Nuku-Sabon Gari da ke yankin Abaji, Mista Peter Yanzu, da wasu mambobin jam’iyyar 157 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Tsohon shugaban matasan yayinda yake jawabi a madadin masu sauya shekar a ranar Laraba a makarantar firamare na Nuku, cewa shi da sauran mambobin suna PDP tun a 1999 amma daga bisani sai jam’iyyar da suka yiwa aiki ta yasar da su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel