Yadda APC ta bani cin hanci don barin PDP amma naki yarda - Tambuwal

Yadda APC ta bani cin hanci don barin PDP amma naki yarda - Tambuwal

- Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya bayyana yadda ya ki karbar wani cin hanci da gwamnatin tarayya ta bashi na gida hanya zuwa kauyensa

- Tambuwal ya yi tsokaci kan yunwar da ta addabi kasar, wanda a cewarsa hakan ya farune sakamakon rashin iya shugabancin Muhammad Buhari

- Tambuwal ya bada tabbacin cewa jam'iyyar PDP zata lashe zabe a kowacce kujera ta jihar Sokoto, domin hukunta APC akan matsatsin rayuwar da ta jefa al'umar jihar

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya bayyana yadda ya ki karbar wani cin hanci da gwamnatin tarayya ta bashi na gida hanya zuwa kauyensa, da nufin rike shi don kar ya bar jam'iyar APC.

Da yake jawabi a wani gangamin yakin zabe a Silame, jihar Sokoto, don kaddamar da yakin zaben jam'iyyar PDP a jihar Sokoto, Tambuwal ya yi tsokaci kan yunwar da ta addabi kasar, wanda a cewarsa hakan ya farune sakamakon rashin iya shugabancin Muhammad Buhari, da kuma gazawa wajen magance matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.

Da yake bukatar masu zabe da su yi waje da gwamnatin APC daga sama har kasa, Tambuwal ya bada tabbacin cewa jam'iyyar PDP zata lashe zabe a kowacce kujera ta jihar Sokoto, domin hukunta APC akan matsatsin rayuwar da ta jefa al'umar jihar.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: An bankado badakalar rashawa a hukumar da surukin Buhari ke shugabanta

Yadda APC ta bani cin hanci don barin PDP amma naki yarda - Tambuwal

Yadda APC ta bani cin hanci don barin PDP amma naki yarda - Tambuwal
Source: Facebook

Da yake nuni da irin yunkurin da akayi don ganin ya zana a APC, Tambuwal ya ce: "Da suka fahimci ina da kudurin barin APC, sai suka yi gaggawar tarbata da cewar zasu gina titi zuwa kauyena tare da rokona akan kar na bar jam'iyyar.

To mu mun fahimci APC ta cusa matsatsin rayuwa ga al'umma, don haka muma sai mun hukuntata, ta hanyar fitowa kwanmu da kwarkwatarmu don zabar PDP tare a yin waje da gwamnatin APC daa sama har kasa.

Saboda sun rasa madafa, shine suka yi karyar cewa wai mambobin jam'iyyar PDP guda 50,000 suka sauya sheka zuwa APC a dan karamin garin nan na Sanata Wamakko. Ta yaya hakan zata faru? Babu yadda zamu dore akan wannan turba, ta wadanda suka lalata dukkanin abubuwan more rayuwa na kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel