Da duminsa: An bankado badakalar rashawa a hukumar da surukin Buhari ke shugabanta

Da duminsa: An bankado badakalar rashawa a hukumar da surukin Buhari ke shugabanta

- Sama da 'yan kwangila 815 ne hukumar BDCA ta sanya sunayensu daga cikin masu aiwatar da ayyukan mazabu, duk da cewar sun gaza cimma bukatun da ake bukata

- Wannan ne karo na biyu a cikin kasa da wata daya da hukumar ke fuskantar zargin handamar kudi da kuma yin nuku nuku a gudanar da ayyukanta

- Akalla 'yan kwangilar zasu samu kudi tsakanin N10m zuwa N200m. Surukin shugaban kasa Buhari, Junaid Abdullahi, shine babban sakataren hukumar

Sama da 'yan kwangila 815 ne hukumar bunkasa garuruwan da ke kusa da iyakokin kasa (BDCA) ta sanya sunayensu daga cikin masu aiwatar da ayyukan mazabu, duk da cewar sun gaza cimma bukatun da gwamnatin tarayya ta gindaya na bayar da kwangilar.

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wani rahoton bincike da jaridar Premium Times ta gudanar kuma ta wallafa. Wannan ne karo na biyu a cikin kasa da wata daya da hukumar ke fuskantar zargin handamar kudi da kuma yin nuku nuku a gudanar da ayyukanta.

Idan har za a sanya sunanka, ya zama wajibi dan kwangilar ya cimma wasu matakai da ke kunshe a cikin jadawalin ka'idoji da gwamnatin tarayya ta wallafa.

KARANTA WANNAN: ASUU: Zamu ci gaba da yajin aiki har sai gwamnatin tarayya ta cika alkawuranta

Da duminsa: An bankado badakalar rashawa a hukumar da surukin Buhari ke shugabanta

Da duminsa: An bankado badakalar rashawa a hukumar da surukin Buhari ke shugabanta
Source: Twitter

Hukumar ta sanar da neman 'yan kwangila don gudanar da ayyukan mazabu akalla 400, wanda kudin aikin yake cikin kasafin 2018.

Hakika zai zama kamar tarnaki idan har hukumomin yaki da cin hanci da rashawa suka gaza gudanar da binciken zargin badakalar da ake yiwa hukumar BDCA, gabanin fara aiwatar da matakan bayar da kudin gudanar da ayyukan.

Akalla 'yan kwangilar zasu samu kudi tsakanin N10m zuwa N200m. Surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Junaid Abdullahi, shine babban sakataren hukumar ta BDCA, wacce aka samar da ita tun 2003.

Hukumar BDCA na da alhakin samar da ababen more rayuwa da bunkasa garuruwan da ke kusa da iyakokin kasar, a cikin jihohi 21 na kasar, da suka hada da kananan hukumomi 105 da ke cikin jihohin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel