Tsohon shugaban matasan PDP da wasu 157 sun sauya sheka zuwa APC a Abaji

Tsohon shugaban matasan PDP da wasu 157 sun sauya sheka zuwa APC a Abaji

- Tsohon shugaban matasa na babbar jam’iyyar adawa PDP a mazabar Nuku-Sabon Gari da ke yankin Abaji, Mista Peter Yanzu ya koma APC

- Ya sauya shekar ne tare da wasu mambobin PDP 157

- Yace tun da jam’iyyar ta yasar da su, sun yanke shawarar yasar dasu, sun yanke hukuncin komawa jam’iyyar APC bayan yawan tattaunawa da wasu tsoffin mambobin PDP a yankin

Tsohon shugaban matasa na babbar jam’iyyar adawa Peoples Democratic Party (PDP) a mazabar Nuku-Sabon Gari da ke yankin Abaji, Mista Peter Yanzu, da wasu mambobin jam’iyyar 157 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Tsohon shugaban matasan yayinda yake jawabi a madadin masu sauya shekar a ranar Laraba a makarantar firamare na Nuku, cewa shi da sauran mambobin suna PDP tun a 1999 amma daga bisani sai jam’iyyar da suka yiwa aiki ta yasar da su.

Yace tun da jam’iyyar ta yasar da su, sun yanke shawarar yasar dasu, sun yanke hukuncin komawa jam’iyyar APC bayan yawan tattaunawa da wasu tsoffin mambobin PDP a yankin.

Tsohon shugaban matasan PDP da wasu 157 sun sauya sheka zuwa APC a Abaji

Tsohon shugaban matasan PDP da wasu 157 sun sauya sheka zuwa APC a Abaji
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa gwambatin APC karkashin jagorancin Alhaji Abdulrahman Ajiya yayi matukar kokari musamman a fannin ababen more rayuwa, ilimi da kuma tallafawa matasa.

KU KARANTA KUMA: Buhari bai da ilimin tattalin arziki – Titi Abubakar

Shugaban APC reshen Abaji, Alhaji Haruna Mohammed Yaba, ya yaba ma tsohon jigon na PDP da tawagarsa da suka dawo APC, cewa kada suyi kasa a gwiwa wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a lokacin zabe.

Ya basu tabbacin cewa za su yi aiki tare da su a duk wani hukunci da za su yanke sannan ya shawarci masu sauya sekar da kada su zamo yan bayan gace, cewa su fito suyi ma jam’iyyar aiki a bayyane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel