ASUU: Zamu ci gaba da yajin aiki har sai gwamnatin tarayya ta cika alkawuranta

ASUU: Zamu ci gaba da yajin aiki har sai gwamnatin tarayya ta cika alkawuranta

- ASUU ta ce ba zata janye yajin aikin da take kan gudanarwa ba har sai gwamnatin tarayya ta cika dukkanin alkawuran da ta daukar mata

- ASUU ta ce babu wata matsaya da aka cimmawa tsakaninta da gwamnatin tarayya a zaman da bangarorin suka yi a ranar Talata

- ASUU ta tariyo cewa ko a karshen 2018, gwamnatin tarayyar ta yi akawarin sakin kudaden don bunkasa ayyukan jami'o'in, amma ta gaza cika alkawarin

Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU, a ranar Alhamis ta ce ba zata janye yajin aikin da take kan gudanarwa ba har sai gwamnatin tarayya ta cika dukkanin alkawuran da ta daukar mata a lokacin da aka yi taron karshe na bangarorin biyu.

Malaman jami'o'in gwamnatin sun ce sun gaji da gafara 'sir' basu ga kaho ba, don haka ba zasu lamunci yadda gwamnatin ke wasa da hankulansu wajen gaza cika alkawarin da kullum take daukar masu, inda suka ce ba zasu janye yajin aikin ba har sai sun gani a kasa.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, a cikin wata tataunawa ta musamman da jaridar Punch a ranar Alhamis a Legas, ya ce babu wata matsaya da aka cimmawa tsakanin tawagar kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya a zaman da bangarorin suka yi a ranar Talata.

KARANTA WANNAN: Buhari ba zai Musuluntar da Nigeria ba, APC ba jam'iyyar Musulmai ba ce - Osinbajo

ASUU: Zamu ci gaba da yajin aiki har sai gwamnatin tarayya ta cika alkawuranta

ASUU: Zamu ci gaba da yajin aiki har sai gwamnatin tarayya ta cika alkawuranta
Source: UGC

Da aka tambaye shi ko zasu janye yajin aikin da suke kan gudanarwa, Ogunyemi ya ce, "Mambobinmu sun ce basa son a janye yajin aikin har sai sun gani a kasa, sai gwamnati ta cika dukkanin alkawura da ta dauka."

A ranar Talata, ASUU ta gana da wakilan gwamnatin tarayya da suka hada da ministan ilimi, Adamu Adamu da kuma takwaransa na kwadago da daukar aiki, Chris Ngige. Bayan kammala taron ne Ngige ya bayyana alkawura da gwamnatin ta daukarwa kungiyar ta ASUU.

Ngige ya bayyana cewa ofishin babban akawu na kasa da kuma ma'aikatar kudi, sun tabbatar da cewa an sakarwa jami'o'i N15.4bn.

Sai dai shugaban ASUU ya tariyo cewa ko a karshen shekarar data gabata, gwamnatin tarayyar ta yi akawarin sakin kudaden don bunkasa ayyukan jami'o'in, amma ta gaza cika alkawarin, don haka ba zasu yarda da wannan alkawari na yanzu ba har sai gwamnatin ta cika.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel