Za a fatattaki Yaran Bukola Saraki da ke cikin Gwamnatin Buhari – Lai Mohammed

Za a fatattaki Yaran Bukola Saraki da ke cikin Gwamnatin Buhari – Lai Mohammed

Mun ji cewa Ministan yada labarai da al’adau na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa za a yi waje da na-kusa da Bukola Saraki da ke rike da mukamai a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Za a fatattaki Yaran Bukola Saraki da ke cikin Gwamnatin Buhari – Lai Mohammed

Lai Mohammed yace Mutanen Kwara sun yi shekaru kusan 50 a hannun su Saraki
Source: Depositphotos

Ministan ta bayyana wannan ne a wajen wani babban taro da jam’iyyar APC ta shirya a jihar Kwara domin Mata. Kamar yadda mu ka samu labari, an wayar da kan Matan da ke goyon bayan APC game da zaben da za ayi.

Lai Mohammed ya zargi shugaban majalisar dattawan na Najeriya, Bukola Saraki, da kokarin kawowa gwamnatin Buhari cikas. Alhaji Lai yace Saraki ya rika amfani da kujerar sa wajen hana ruwa gudu a gwamnatin APC.

Sai dai duk da haka, har yanzu akwai manyan mukarraban shugaban majalisar a cikin gwamnati. Ministan kasar yace gwamnatin shugaba Buhari ba za tayi sanya wajen korar irin wadannan mutane daga bakin aiki ba.

KU KARANTA: Buhari ya mika ta’aziyyar sa bisa rasuwar wani babban Basaraken Arewa

Mohammed yace mutanen da Saraki ya kawo daga jihar Kwara aka sa cikin ma’aikatu da hukumomin gwamnati su na nan rike da mukaman su alhali yana zargin cewa shugaban kasa Buhari yayi watsi da mutanen jihar Kwara.

Alhaji Mohammed ya koka da yadda gidan su Saraki su kayi shekara 40 zuwa 50 su na mulkin jihar Kwara. Mohammed ya bayyana cewa mutanen jihar ba za su cigaba da bari a rika yi masu wannan dan-waken-zagaye a 2019 ba.

Daga cikin wanda su ka halarci wannan taro kuma har su kayi jawabi a wurin akwai Hajiya Rahmat Okin-Abolaji, wanda tana cikin jagororin matan APC a jihar. An shirya taron ne jiya a cikin Garin Ilorin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel