Za mu doke APC kamar yadda aka gani a zaben Kasar Congo – PDPCO

Za mu doke APC kamar yadda aka gani a zaben Kasar Congo – PDPCO

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar adawa a Najeriya watau PDP, ta kara bada tabbacin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya fara shirin shan kasa a babban zaben da za ayi.

Za mu doke APC kamar yadda aka gani a zaben Kasar Congo – PDPCO

Buhari ya shirya shan kashi a hannun Atiku inji PDP
Source: Twitter

Jam’iyyar hamayya ta PDP tace abin da ya faru a kasar Congo zai faru a wata mai zuwa a Najeriya, inda ‘dan takarar jam’iyyar da ke mulki watau Emmanuel Ramazani Shadary ya sha kashi a hannun jam’iyyar adawa a kasar ta Afrika.

Kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar na PPCO ta fitar da jawabi ta bakin Darektan ta na yada labarai, Kola Ologbondiyan, inda tace zaben da aka yi a Congo ya ba ta karfin gwiwa wajen ganin ta lallasa APC a zaben mai zuwa.

KU KARANTA: Atiku ya zargi Buhari da kwashe kudin gwamnati domin yakin neman zabe

Jam’iyyar PDP tace duk da shirin da APC ta ke yi na murde zabe, ba ta jin wannan zai hana ta yin nasara. Jam’iyyar adawar ta tunawa jama’a yadda Julius Maada Bio ya doke jam’iyyar adawa a kasar Sierra Leone a shekarar bara.

Haka kuma a 2017, George Weah ya doke mataimakin shugaban kasar Liberia, Joseph Boakai, a takarar da su kayi. A karshen 2016 ne kuwa, ana ji ana gani Nana Akufo-Addo ya doke shugaba John Mahama ya karbi mulkin kasar Ghana.

PDP ta taya sabon shugaban kasar Congo da za a rantsar, Felix Tshiekedi nasarar lashe zabe, inda ta ce a Ranar 16 ga Watan Fubrairu mutanen Najeriya musamman wadanda su ka rasa aikin su a gwamnatin APC za su yi waje da Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel