Buhari yayi magana game da zargin da ke wuyan Gwamnan Kano Ganduje

Buhari yayi magana game da zargin da ke wuyan Gwamnan Kano Ganduje

Mun samu labari daga jaridar Daily Nigerian cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi magana game da zargin da ke kan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, na karbar cin hanci da rashawa.

Buhari yayi magana game da zargin da ke wuyan Gwamnan Kano Ganduje

Ana zargin Ganduje da karbar rashawa daga hannun ‘yan kwangila
Source: Twitter

Kamar yadda labari ya zo mana, an sake bijirowa da wannan batu ne a lokacin da aka kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari na APC. A wajen babban taron an tsara yadda APC za ta shirya jadawalin kamfen din ta.

Wani daga cikin wadanda ke cikin wannan kwamiti kuma tsohon Sanatan Kano watau Bashir Lado ya nemi shugaba Buhari yayi kamfe a Legas da Kano a daf da lokacin da za a rufe yakin neman zabe saboda dinbin jama’ar yankin.

KU KARANTA: Kwankwaso ya caccaki Gwamnan Kano game da zargin karbar rashawa

Sai dai shugaban kasar ya maidawa tsohon Sanatan martani cikin raha da cewa yana gudun mutanen Kano su yi masa magana game da Ganduje wanda aka gani a bidiyo yana karbar makudan daloli na rashawa yana murmushi.

Shugaba Buhari yace idan har mutane su kayi masa maganar gwamna Ganduje, bai san abin da zai fada masu ba. Shugaban kasar yake cewa sam ba zai yi kamfe a jihar Kano ba har sai idan ya zama masa dole saboda wannan zargi.

Kwanaki kun ji labari cewa Uwargidar shugaban kasa watau Hajiya Aisha Buhari ta tashi tayi tafiyar ta a lokacin da gwamna na Kano ya fara jawabi a lokacin da aka yi wani taron APC a jihar Kano.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel