Buhari ya mika ta’aziyyarsa bisa rasuwar wani babban basarake daga yankin Arewa

Buhari ya mika ta’aziyyarsa bisa rasuwar wani babban basarake daga yankin Arewa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa bisa rasuwar mai martaba Sarkin Lafia, Alhaji Isah Mustapha Agwai I, da ya rasu da yammcin ranar Alhamis 10 ga watan Janairu, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Legit.com ta ruwaito Buhari ya bayyana alhinin nasa ne cikin wata sanarwar da babban mashawarcinsa akan al’amuran watsa labaru, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, inda ya jajanta ma iyalan marigayin.

KU KARANTA: Atiku ya zargi Buhari da APC sun kwashe kudin gwamnati suna yakin neman zabe dasu

Buhari ya mika ta’aziyyarsa bisa rasuwar wani babban basarake daga yankin Arewa

Sarkin Lafiya
Source: UGC

Haka zalika sanarwar ta mika ta’aziyyarta ga gwamnan jahar Nassarawa, Umaru Tanko Al-Makura, da kuma majalisar Sarkin Lafia, jama’an garin Lafia da ma al’ummar jahar Nassarawa gaba daya kwata bisa wannan babbar rashi da suka tafka na Sarki Agwai.

Shugaba Buhar ya kuma jaddada tausayawarsa ga Iyalan mamacin, gwamnan jahar Nassarawa, masarautar Lafiya, al’ummar garin Lafiya, a daidai lokacin da suke jimamin rashin Sarki Agwai, wanda har rasuwarsa shine shugaban majalisar sarakunan gargajiya da kuma kungiyar Jama’tul Nasril Islam.

Sanarwar ta kara da cewa ba za’a manta da Sarkin ba musamman ta yadda ya gudanar da mulki nagari, da kuma jajircewarsa wajen ganin ya inganta rayuwar al’ummarsa tun bayan darewarsa kujerar Sarki a shekarar 1974.

A shekaru Arba’in da hudu (44) da sarkin ya kwashe a saman karagar mulki ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakanin addinai mabanbanta, halin yafiya, da kuma sulhunta tsakanin bangarori masu rikici da juna, tare da kuma ciyar da sha’anin ilimi gaba.

Daga karshe Buhari ya yi addu’ar Allah Ya jikan mamacin, tare da fatan mutuwa ta zamto hutu a gareshi, hakanan yayi addu’ar Allah Ya zaba ma jama’an masarautar Lafiya jagora nagari. Za ayi jana'izar Sarki Agwai a ranar Juma’a a garin Lafia.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel