Atiku ya zargi Buhari da APC sun kwashe kudin gwamnati suna yakin neman zabe dasu

Atiku ya zargi Buhari da APC sun kwashe kudin gwamnati suna yakin neman zabe dasu

Dan takarar jam’iyyar PDP a mukamin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya zargi abokin karawarsa daga jam’iyya mai mulki, jam’iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari da kwasan kudin al’umma suna hidimar gabansu.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Atiku Abubakar yana fadin cewa Buhari da jam’iyyar APC suna amfani da kudaden gwamnati wajen gudanar da yakin neman zabe don ganin sun kayar dashi a zaben shugaban kasa da za ayi a ranar 16 ga watan Feburarun 2019.

KU KARANTA: Ibtila’I ya auku a jahar Legas, hatsarin jirgi ya rutsa da jama’a da dama

Hakan kuma yi ma dokokin kundin tsarin mulki na da dokokin zabe karan tsaye ne, kamar yadda kaakakin Atiku, Paul Ibe ya bayyana a wata ganawa da yayi da manema labaru a ranar Alhamis 10 ga watan Janairu.

A sanarwar daya fitar, Paul, ya bayyana cewa a watan Disambar shekarar data gabata ne shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya gargadi masu rike da mukaman siyasa dasu guji amfani da arzikin gwamnati wajen yakin neman zabensu, ko kuma amfani dasu wajen yakar abokan hamayyarsu.

Paul Ibe yace yana magana ne ta yadda ma’aikatan watsa labaru da al’adun gargajiya take watsa wasu bidiyo a gidajen talabijin da sun tallata gwamnatin shugaba Buhari, wanda yace hakan ya saba ma dokokin zabe na shekarar 2010.

A cikin wadannan bidiyo, ana nuna wasu ayyukan cigaba da ake dangantasu ga gwamnatin shugaba Buhari, wanda aka ce ya yi su ne a jihojin Abia, Kwara, Lagos, Ebonyi, Delta, Kano da sauran jihohin Najeriya.

Daga karshe Mista Paul ya yi kira ga hukumar INEC da ta lissafa kudin da aka kashe wajen shirya wannan talla, ta sanya shi cikin naira biliyan daya da dokokin zabe suka iyakance ma dan takarar shugaban kasa ya kashe wajen yakin neman zabe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel