Korarrun ma’aikatan da El-Rufai ya sallama 9,000 na ta fafutukar ya biyasu hakkokinsu

Korarrun ma’aikatan da El-Rufai ya sallama 9,000 na ta fafutukar ya biyasu hakkokinsu

Akalla tsofaffin ma’aikata su dubu tara da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sallama daga aiki na fafutukar ganin sun samu hakkokinsu daga gwamnatin hara yanzu bayan sama da shekara guda daga barin aiki.

A shekarar 2017 ne dai gwamnatin jahar Kaduna ta sallami ma’aikatan, sai dai har yanzu basu samu hakkokin da ya kamata gwamnati ta biyasu ba kamar yadda suka tabbatar ma duniya ta bakin sakataren kungiyarsu, Ahmed Mu’azu.

KU KARANTA: Ibtila’I ya auku a jahar Legas, hatsarin jirgi ya rutsa da jama’a da dama

Kaakakin kungiyar tsofaffin ma’aiakatan da garambawul a tsarin aikin gwamnatin jahar Kaduna ya shafa, Ahmed Muazu ya bayyana ma manema labaru cewa sun yanke shawarar yin karin haske ne game da batun da gwamnan ke yadawa na cewa wai ya biya yan fansho hakkokinsu.

“Ya zama dole mu yi karin haske duba da maganganun da Gwamna El-Rufai ke yawan furtawa game da hakkokin yan fansho, inda yace cewa ya kammala biyan kowa da kowa, muna shiga cikin rudani a duk lokacin da muka ji gwamnan ya yi irin wannan furuci.

“Da wannan muke sanar da jama’a, tare da kuma girmamawa ga mai girma Gwamna El-Rufai dake yawan bayyana ma duniya cewa duk yan fansho sun samu kudadensu, cewa har yanzu mu kam bamu samu namu hakkokin namu ba.

“Kuma muna kira ga gwamnan ko kuma duk wanda yake ganin wallenmu daya binciki kamfanonin fanshon da muka yi rajista dasu don binciken ko akwai mutum daya daga cikin mu dubu tara da gwamnati ta biya hakkokinsa, kullum sai dai su ce mana suna jiran gwamna.” Inji shi.

A cewar Muazu, yawancin tsofaffin ma’aikatan sun kwashe tsawon shekaru masu yawa suna aiki, wasu daga ma ciki ma sun kai mukamin darakta ko mataimakin darakta, a yanzu haka sun fara gajiya da jira, wasu ma sun mutu, wasu kuma na fama da cututtukan hawan jini da na mutuwar rabin jiki, da sauran jarrabi na rayuwa daban daban.

Sai dai duk kokarin da majiyar Legit.com tayi na jin ta bakin kaakakin gwamnatin jahar Kaduna, Samuel Aruwan ya ci tura, sakamakon baya amsa wayarsa, kuma bai amsa sakon kota kwana da aka tura masa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel