Soji na neman bayanai kan duk wasu da ake zargi da ta'addanci ko Boko Haram

Soji na neman bayanai kan duk wasu da ake zargi da ta'addanci ko Boko Haram

- Jami'an sojin kasar nan sun bayyana duk wani motsi na Boko haram

- Wasu daga cikin yan boko haram din sun kutsa cikin kauyukan dake jihar ta Maiduguri

- Colonel Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wani rahoto daya fitar a ranar Alhamis

Soji na neman bayanai kan duk wasu da ake zargi da ta'addanci ko Boko Haram

Soji na neman bayanai kan duk wasu da ake zargi da ta'addanci ko Boko Haram
Source: Twitter

A kokarin kawo karshen ta'addancin yan boko haram a cikin Maiduguri jami'an sojin kasar nan sun bayyana cewa kungiyar tana neman hanyar da zata kara karfi ta hanyar tsorata al'umma.

Wasu daga cikin yan ta'addan boko haram din sun fantsama sun shiga cikin kauyukan dake jihar ta Maiduguri.

Colonel Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wani rahoto daya fitar a ranar Alhamis inda yake cewa

GA WANNAN: An haramta amfani da mayukan bilicin masu haskaka fata a kasar Rwanda

"Suna tsorata al'umma da kuma ja musu kunne akan suba muhallin su".

Ya kara da cewa "da dama daga cikin wadannan mutane sun bar gidajen su,muna sanarwa da al'umma cewa duk wanda ya kuma zuwa yayi musu barazana suyi kokarin sanar da hukumar".

"Rashin sanarwar zai nuna kamar cewa ana goyan bayan yan ta'addan ne sannan duk wanda muka kama da hakan zamu hukuntashi kamar yanda zamu hukunta yan boko haram din.

Saboda haka muna neman goyan baya al'umma dan kawo karshen wadannan mutane

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel