Yanzu kau mun tsarkaka, duk mugayen sun koma jikin Buhari - PDP ga 'yan Najeriya

Yanzu kau mun tsarkaka, duk mugayen sun koma jikin Buhari - PDP ga 'yan Najeriya

- Jam'iyar PDP tace yanzu ta tsarkaka saboda duk wasu masu cin dukiyar gwamnati sun koma APC

- Jam'iyar APC itace jagaban jam'iyu a bangaren cin rashawa

- Jam'iyar ta bayyana haka ne a lokacin da suke gudanar da wani taro da mabiya cocin Pentecostal suka shirya

Sharuddan Saudiyya ga Najeriya kan hajjin 2019

Sharuddan Saudiyya ga Najeriya kan hajjin 2019
Source: Twitter

Bayan da 'Barayin PDP' ke ta arcewa daga jam'iyyar ana dab da zabukan kasa, PDP tace yanzu kau ta tabbata sun fi jam'iyya mai mulki tsarki, tunda duk masu kashi a gindi sun tsere inda zasu tsira daga hukunci, don haka ayi wa Allah a zabe su.

Jam'iyar PDP tace a halin yanzu jam'iyar su ta zama tsarkakakkiya saboda duk wasu masu cin dukiyar gwamnati sun fita a PDP sun koma APC.

Jam'iyar ta bayyana hakan ne a wani taro da ya gudana a Ikeja wanda mabiya cocin Pentecostal suka shirya.

GA WANNAN: EFCC tayi ram da mai gadin ATM da aka ga N30,000,000 a asusunsa

Jam'iyu da dama da suka samu halartar wannan taro sun tofa albarkacin bakin su sannan sun bayyanawa shuwagabannin kiristocin kudirorin su.

Taron ya samu halartar shugaban hukumar zabe na kasa da kuma kungiyar nan ta gabashin Asia.

PFN yace zasu sanya ido sosai akan zaben sannan zasu sanya wakilai guda Biyar a kowanne gurin kada kuri'a a jihar ta Legas.

A wajen taron jam'iyar PDP tace ta kore duk wasu bara gurbi daga cikin su sun koma APC.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel