Amo daga Amurka: Karku zabi Atiku, arzurta dangi da abokai zayyi

Amo daga Amurka: Karku zabi Atiku, arzurta dangi da abokai zayyi

- Wata kungiyar Amurka tace matukar Atiku yaci zabe zai maida hankali gurin azurta kanshi

- Kamar yanda rahoton kungiyar ya bayyana, Atiku na da iyayen gida

- Shine babban kalubalen shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa

Amo daga Amurka: Karku zabi Atiku, arzurta dangi da abokai zayyi

Amo daga Amurka: Karku zabi Atiku, arzurta dangi da abokai zayyi
Source: Facebook

Dan takarar shugabancin kasa karakashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, zai azurta kanshi da abokan shi ne matukar ya samu nasarar zaben 2019 inji wata kungiya ta Amurka a rahoton shekarar 2019 na kungiyar.

"Manya ne ke mulkar shi kuma zai maida hankali gurin azurta kanshi da abokan shi tare da gujewa aiyukan shi na dole a matsayin shi na shugaba."Kamar yanda kungiyar Eurasia ta wallafa a rahoton ta na 7 ga watan Disamba.

Amma kuma kungiyar goyon bayan Atiku tace " saboda lafiyar shi da hazakar shi" idan aka danganta shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dan takarar jam'iyyar APC, "zai habako da tattalin arzikin kasar nan da gaggawa."

"Amma kuwa hakan zai kara durkusar da tattalin arzikin kasar nan," inii kungiyar.

GA WANNAN: Bayan su Shehu Sani sunyi wa El-Rufai 'buqulu' shi kau Bindow bankin duniya ya bashi biliyoyi

Kungiyar Eurasia ta fitar da rahoton hatsarirrika manya guda goma inda ta sa Najeriya a lamba ta goma tare da maida hankali akan zaben watan Fabrairu na 2019 mai zuwa.

Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya na shekaru 8 zai kara da yan takara 59 akan kujerar shugabancin kasa.

Amma kuma babban abokin adawar shi shine shugaban kasa Muhammadu Buhari. Abubakar, bayan barin APC zuwa PDP a karshen 2017, ya zamo babban kalubale ga Buhari ballantana ma ta fuskar tattalin arziki.

Abubakar yana ikirarin cewa sanin makamar mulki da kasuwancin shi sune abinda kasar ke bukata, karawa da ganin yanda ya tsaya a harkar habakar tattalin arziki karkashin shugabancin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel