Karin bayani daga Jaridar Vanguard kan wai ana tsaka da Kanfe Tinubu ya yanke jiki ya fadi aka kuma garzaya dashi asibiti

Karin bayani daga Jaridar Vanguard kan wai ana tsaka da Kanfe Tinubu ya yanke jiki ya fadi aka kuma garzaya dashi asibiti

- Labarin da suka wallafa akan Tinubu da jam'iyyar APC ba gaskiya bane

- Tinubu na nan lafiya kalau

- Suna bada hakuri akan kunci ko tozarcin da labarin ka iya jawowa gareshi da jam'iyyar shi

Limamin Coci zai dauki Almajirai ya koya musu sana'a, Limaman Musulmi sunce anqi wayon

Limamin Coci zai dauki Almajirai ya koya musu sana'a, Limaman Musulmi sunce anqi wayon
Source: UGC

Garin azarbabin sakin labari, jaridar Vanguard, mai fidda labaranta a jaridu da ma yanar gizo a fadin Najeriya, tayi wata katobara inda tace Bola Ahmed Tinubu na can rai ga hannun Allah, a asibiti, bayan ya yanke jiki ya fadi a filin gangamin siyasa.

A yanzu dai sun tabbatar wannan labaran karya ne, kuma suna neman afuwar Bola Tinubu Jagaban yankin yammacin Najeriya, bayan sun gano ashe kanzon kurege ne da Fake News.

Asali dai FAni Kayode, mai babatu da yawun PDP ne ya wallafa labarin sai dai shi dama an saba jin farfaganda irin wannan a bakinsa shekaru 5 kenan, kuma bai taba fuskantar tuhuma kan hakan ba.

GA WANNAN: Obi Ezekwesili na ci gaba da ragadinta kasuwanni da gidaje

Ga rubutun neman afuwar tasu: A ranar 10 ga watan Janairu, 2019 mun wallafa a yanar gizo cewa "Tinubu ya yanke jiki ya fadi, a yanzu yana aibiti bayan an zabe shi shugaban yakin neman zaben Buhari, inji Fani Kayode" wanda kadan daga cikin abubuwab da aka wallafa akan shugaban jam'iyyar APC kuma shugaban yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari.

'Tuni muka gano rashin ingancin labarin. A don haka ne muke muke karyata labarin tare da bada hakuri ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da kuma jam'iyyar APC akan kunci da tozarci da labarin zai iya jawo musu".

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel