Kotu ta ci gaba da sauraren kara ba tare da bayyanar Dasuki ba

Kotu ta ci gaba da sauraren kara ba tare da bayyanar Dasuki ba

Yayinda ake ci gaba da shari’ar tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Sambo Dasuki, a jiya Laraba, 9 ga watan Janairu, Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama Abuja, ta ci gaba da shari’a ba tare da bayyanar wanda ake kara a kotun ba.

Ana tuhumar Dasuki ne tare da Bashir Yuguda, Dalhatu Investiment Limited, Sagir Attahiru da kuma Attahiru Bafarawa a bisa zargin karkatar da kudade kimanin naira bilyan 19.4.

Tun a shekarar 2015 dai ake tsare da Dasuki, duk da cewa kotu ta bayar da umarnin a sakin shi a bisa beli.

Cikin 2018 ne Dasuki ya ce ba zai sake zuwa kotu ba, tunda ita ma gwamnatin tarayya ta bijire wa umarnin kotu, ta ki sakin sa a kan beli.

Kotu ta ci gaba da sauraren kara ba tare da bayyanar Dasuki ba

Kotu ta ci gaba da sauraren kara ba tare da bayyanar Dasuki ba
Source: Depositphotos

A jiya Laraba, lauyan huumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) Oluwaleke Atolagbe, ya shaida wa kotu cewa mai gabatar da shaida ya na kotun, kuma a shirye ya ke ya bayar da shaidu na hujjoji.

KU KARANTA KUMA: Kin halaratar taron PDP: Mataimakin gwamna a jihar kudu ya dakatar da albashin manyan jami'an gwamnati

Amma Atolagbe ya ce ba za a iya ci gaba da, tunda Dasuki bai yarda an kawo shi kotun ba.

Shi kuma lauyan Dasuki mai suna Victor Okudili, ya nemi kotu a dage shari’ar har sai yadda hali ya yi, kuma sai EFCC ta bi umarnin Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu, wadda ta bayar da belin Dasuki tun a ranar 2 ga watan Yuli, 2018.

Mai Shari’a Hussain Baba-Ahmed ya dage sauraren sai ranar 19 ga watan Fabrairu domin ya san hukuncin da zai yanke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel